Yadda za a lura da fata mai gautsi

Idan mace tana da fata mai gautsi, to tana tattare da babbar matsala, saboda duk wanka ko kwalliya ba zai fitar da kyawunta ba. Gautsi na rage wa mata farin jini a wurin jama’a. Don haka ne muka kawo muku yadda za a magance matsalolin fata mai gautsi.·         A samu zuma da ‘ya’yan itacen strawberry […]

Yadda za a lura da fata mai gautsi

Idan mace tana da fata mai gautsi, to tana tattare da babbar matsala, saboda duk wanka ko kwalliya ba zai fitar da kyawunta ba. Gautsi na rage wa mata farin jini a wurin jama’a. Don haka ne muka kawo muku yadda za a magance matsalolin fata mai gautsi.
·         A samu zuma da ‘ya’yan itacen strawberry (za a iya samun wannan ’ya’yan itacen a manyan shaguna). Strawberry na dauke da sinadarin bitamin C. inda zuma take warkar da cututtuka. A daka ‘strawberry’ guda uku, sannan a hada da zuma cokali daya. A shafa a jiki da fuska kullum kafin a yi wanka. Za a wanke bayan minti 15.
·         Shan shayi mai dauke da ganyen ‘pepper mint’ na taimaka wa jini zaga jiki cikin sauki, shan wannan shayi na wanke maikon da ke makale wadanda suke hana fata sheki.
·         Za a iya samun lemon tsami da jar albasa ba fara ba. A yanka albasar, sai a markada, sannan a zuba ruwan lemon tsami a cikin markadaddiyar albasa. Daga nan a shafa a jiki da fuska. A jira tsawon minti 10 zuwa 15 kafin a wanke, domin samun sakamako mai gamsarwa.
·         Idan fata na dauke da bakin kunar rana, sai a rika amfani da mayuka masu dauke da ‘sunscreen’, ko kuma a samu bakar soda (za a iya samun ta a shagunan da ake sayar da kayan yin kek). A zuba cokali kamar 4 na wannan sodar a ruwan dumi. Sai a jika tawul a rika tsomawa ana shafawa a wurin da ya yi baki.