Yadda za a magance fata mai yawan kaikayi

Akwai dalilai da dama wadanda ke haifar da kaikayin fata wadda ke feso da kuraje bayan an yi susa. Yawan kaikayin fata na kasancewa makero ne ko kuma kyasbi da dai cututtukar fata. Yawan kaikayin fata na haifar da kuraje wadanda ke bata fatar fuska. Idan kuraje kuma suka yi yawa, duk irin kwalliyar da […]

Yadda za a magance fata mai yawan kaikayi

Akwai dalilai da dama wadanda ke haifar da kaikayin fata wadda ke feso da kuraje bayan an yi susa. Yawan kaikayin fata na kasancewa makero ne ko kuma kyasbi da dai cututtukar fata. Yawan kaikayin fata na haifar da kuraje wadanda ke bata fatar fuska. Idan kuraje kuma suka yi yawa, duk irin kwalliyar da aka caba a fuskar ba za ta yi kyau ba. Hakan ya sanya a yau na kawo muku irin hanyoyin da za a bi domin magance fata mai kaikayi.

• Idan fatar fuska ko ta jiki tana kaikayi, a samu kankara a rika shafawa a inda ke kaikayin na tsawon minti goma ko kuma har sai kaikayin ya tsaya sannan a daina. Yin hakan yana sanya saukin kaikayin a fuska.

• A samu alkama sannan a tafasa. Bayan ta huce sai a shafa a fuska na tsawon minti ashirin zuwa talatin kafin a wanke.

• Ya kasance ana amfani da man jiki wadanda ke hana fesowar kuraje da kuma hana fata yawan kaikayi.

• A daina amfani da man shafawa wanda yake dauke da kanshin turare.

•A rage shiga cikin rana a lokacin da ta yi zafi sannan kada a cika sosa fatar domin hakan na kara sanya wata cuta a cikin fata.

•A rika amfani da ruwan ganyen ‘aloe bera’ a kan kurajen ko wajen da ke kaikayi sannan a bari na tsawon minti talatin kafin a wanke.

•A yawaita shan ruwa domin idan an sha ruwa yakan wanke magudanar zufa sannan ya hana su toshewa yadda za su rika numfasawa.

•Ya kasance ana amfani da man kwakwa ana shafawa a daidai inda ake jin kaikayin ko kuma a kan kurajen.