Yadda za a magance fitowar gemu a fuskar mace
Shawara ita ce kada a yi amfani da wani man kanti ko wani sabulu.
Sallama gare ku tare da fatan alheri.
Gemu ga ’ya mace na daya daga cikin abubuwan da ke bata fuska da kuma kwalliyarta. Domin yana bata mata adonta.
Sai a ga duk hoda da fandesho da aka sa ba sa kawar da hakan.
Don haka ne a yau na kawo muku hanya mafi sauƙi wadda za a bi domin magance fitar gemu a fuskar ‘ya mace.
- An Kama Dan Sandan Da Ya Harbe Mai Talla A Kasuwar Abuja
- Ramadan: Hisbah ta kama marasa Azumi 12 a Kano
· Za a iya rabuwa da gemun idan an yi amfani da man cire gashi a jiki kamar (hair remobal cream). Sannan a samu auduga a jika da ruwa a goge wajen da aka cire gemun.
·Kurkum na kara taimakawa bayan an cire gashin wajen sai a shafa shi domin kada ya nuna alamar cire gashi daga inda gemun ya fito.
·Yana da kyau a kwaba kurkum da zuma sannan a shafa a fuska kafin a kwanta barci. Yin haka na kare fuska daga sake fitowar wani gashin.
·Amfani da nikakken karas da nono ko madara na kara gyara inda gashin ya fito.
Domin rabuwa da irin wannan matsalar ta hanyar sauki, shawara ita ce kada a yi amfani da wani man kanti ko wani sabulu.
A yi amfani da wadannan bayanan da na bayar don samun biyan bukata.