Yadda za a magance kaushin fata

Kaushin fata abu ne wanda ke addabar fatar mutum musamman a lokacin sanyi. Akwai ababen da ke sanya kaushin fata kamar yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi. Akwai nau’o’in mai da dama masu magance matsalar  kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada. Domin bin hanya mafi sauki wajen magance […]

Yadda za a magance kaushin fata

Kaushin fata abu ne wanda ke addabar fatar mutum musamman a lokacin sanyi.

Akwai ababen da ke sanya kaushin fata kamar yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi. Akwai nau’o’in mai da dama masu magance matsalar  kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada.

Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wannan matsala ta fata sai ku karanta ababen da na lissafo kamar haka:

*  A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a bar ta na tsawon minti biyar zuwa goma kafin a shiga wanka a kullum.

* A rika diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.

* Za a iya kwaba fiya a shafa a jiki a bari na tsawon minti 15 sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada jus din fiya a rika sha domin magance kaushin fata.

* A rika amfani da man kwakwa a fatar jiki. A dora man kwakwa a wuta ya dan yi dumi sannan a mulke fatar jiki na tsawon minti 30  kafin a shiga wanka . A rika yin haka a kullum.

* Shan madara kofi daya kafin a kwanta barci kullum yana taimaka wa fata sosai.

* A rika shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka da dare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gaba daya da man kadanya domin samun fata mai laushi kuma mai sheki.

* A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sannan a shafa a fuska ko fata na tsawon minti 20 sannan a wanke da ruwan dumi.

* Lemun tsami da sukari na taimakawa wajen fitar da fatar da ke da gautsi a jiki sannan suna sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti uku sannan a wanke.

* A yi amfani da daya daga cikin ababen da na lissafo. Kada a shafa a lokaci guda don amfani da abubuwa da yawa na haifar da kuraje.