Yadda za a magance kodewar fata

Kodewar fata na aukuwa ne a lokacin da mutum ya kasance yana yawan shiga cikin rana domin neman halaliyarsa ko kuma don yini a rana. Idan hakan ta kasance, sai fatar ta zama baka. Wannan abu ya fi aukuwa ne a fuska. Sai a ga fuskar gefe daya ta yi baki daya gefen kuma da […]

Yadda za a magance kodewar fata

Kodewar fata na aukuwa ne a lokacin da mutum ya kasance yana yawan shiga cikin rana domin neman halaliyarsa ko kuma don yini a rana. Idan hakan ta kasance, sai fatar ta zama baka. Wannan abu ya fi aukuwa ne a fuska. Sai a ga fuskar gefe daya ta yi baki daya gefen kuma da dan haske. Wannan abu ba a sanin lokacin da suke faruwa. Shi ya sa a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi don neman kariya daga wadannan kunar ranar ko kuma kodewar fata.

• Ruwan dankalin turawa; a fere dankalin turawa sannan a wanke sai a kankare a matse ruwan sannan a rika shafawa a fuska musamman inda fatar ta kode. Yin haka na magance matsalar fatar sannan kuma yana kare sake aukuwar hakan.

• Madara ; a samu madara a sanya a gidan sanyi har sai ta yi sanyi sosai sannan a samu tawul karami a rika tsomawa ana goge fuskar da shi. Madara na sanya hasken fata sannan kuma tana warkar da wannan kodewar fatar.

• Ruwa; a yawaita shan ruwa sosai idan ana dauke da wannan matsalar sannan za a iya sanya ruwan ya yi kankara sannan a rika shafa wannan kankarar a inda fatar ta kode.

•Gurji; a samu gurji sannan a yanka sannan a sanya a gidan sanyi har sai ya yi kankara sannan a rika shafawa a wannan wajen da fatar ta kode ko kuma a rika daurawa wurin har sai ya narke.

• Koren ganyen shayi; za a iya tafasa koren ganyen shayi hade da na’ana. Bayan sun tafasa sannan a bari hadin ya jiku kamar na tsawon sa’a daya  sannan a sanya a gidan sanyi, sannan a wanke fuskar da hadin ko kuma a samu auduga ana shafawa a inda fatar fuskar ta kode.

• Ganyen ‘aloe bera’; a samu wannan ganyen sannan a matse ruwan da ke ciki a rika shafawa a fuskar a kullum har sai kodewar ta yi sauki. Wannan ganye na da matukar mahimmanci a fatar mu don haka yana da kyau a kowane gida a shuka.

• Ruwan tuffa; za a iya samun wannan ruwan ne bayan an kankare sannan a matse. Sai a rika shafawa a fuska har sai ya bushe. Haka za a rika yi a kullum.

• Masu karatu kada su hada duka wannan hadin su ce za su yi shi a lokaci guda. Sai dai su zabi daya daga cikinsu. Hada wadannan ababen da na lissafo na iya haifar da wata cutar fatar fuska. Da fatan za a kiyaye.