Yadda za a magance kurajen fuska ko maruru da wuri

Sau da yawa za a ga mace tana shirin zuwa gidan biki amma, da wayewar gari sai ta ga kuraje sun feso mata ko kuma karamin maruru saboda zafin gari. To, yaya za ta magance wadannan matsaloli da wuri kafin lokacin biki? Don haka ne a yau na kawo muku yadda za a magance wadannan […]

Yadda za a magance kurajen fuska ko maruru da wuri
Yadda za a magance kurajen fuska ko maruru da wuri

Sau da yawa za a ga mace tana shirin zuwa gidan biki amma, da wayewar gari sai ta ga kuraje sun feso mata ko kuma karamin maruru saboda zafin gari. To, yaya za ta magance wadannan matsaloli da wuri kafin lokacin biki? Don haka ne a yau na kawo muku yadda za a magance wadannan matsalolin da wuri.
• Ta samu bawon lemun zaki sai ta markada shi da ruwa kadan, sannan sai ta shafa a kan kurjin da ya feso mata ko maruru.
• A samu tafarnuwa sai a dan daka ta kadan sannan a shafa a kan kurjin yin hakan na batar da tabon kurajen ko na marurun da suka fito.
• Man gyada cokali daya da ruwan lemun tsami na kare fuska daga fesowar kuraje. Don haka ana son a rika shafa wannan hadin a fuska.
• A markada gwanda tare da bawonta sai a shafa a inda kurjin yake. Wannan hadin na rage kumburin fuska.
• Ana wanke fuska da ruwan lemun tsami da tafasashshen  nono don hana kurajen fuska fitowa.
• A shafa ruwan nunannen  tumatiri a fuska ko a kan kurji kamar na tsawon awa daya sannan a wanke.
•Markadadden dankalin Turawa na magance maruru da kurajen fuska da kuma gishirin fuska.
•A samu ruwan rose water sai a kwaba ta da garin sandal sannan a shafa a fuska na tsawon mintuna 20 zuwa 30 sannan a wanke da ruwan dumi.
• Markadadden garin ridi da ruwa na hana kurajen fuska fitowa da kuma kurajen fata.
• A hada ganyen dalbejiya (ko dogon yaro ko neem) da garin kurkum sai a shafa a fuska. Yin hakan na korar da kurajen fuska.