Yadda za a magance maikon fuska

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawu muku guzurin bayani kan yadda za ku yi amfani da madara wajen magance maikon fuskarku. Ku fahimta yawan shan madara na kara lafiyar jiki, tana sanya fata ta rika sheki, ta sanya ta taushi da […]

Yadda za a magance maikon fuska

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawu muku guzurin bayani kan yadda za ku yi amfani da madara wajen magance maikon fuskarku.

Ku fahimta yawan shan madara na kara lafiyar jiki, tana sanya fata ta rika sheki, ta sanya ta taushi da kuma santsi. Hakan ya sanya na kawo muku yadda ya kamata ku yi amfani da madara wajen magance maikon da ke fuskarku.

Abubuwan bukata
. Madara
. Gishiri
. Ruwa
. Auduga
. Zuma
Amfanin madara wajen magance maikon fuska:
•         Madara na goge daudar fuska: A samu madara rabin kofi, sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri, sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke. Daga nan a shafa a fuska da wuya zuwa minti 2 ko 3 kafin a wanke da ruwan dumi.
•         Madara na sanya fata santsi, don haka za a iya amfani da ita a matsayin sinadarin ‘cleanser’. Da farko a samu auduga, sai a tsoma a cikin madarar ruwa, daga nan a rika goge fuska da ita. Daga nan a jira ta bushe kafin a wanke.  Yin hakan na rage maikon fuska, kuma zai sanya fuska ta yi taushi da santsi.
•         Za a iya amfani da madara don kara wa gashi karfi, musamman lokacin sanyi da gashi yakan tsinke. A zuba madara a kan gashi a cuda har ta taba tsagun kai, sai a jira na minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.
•         Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin haka na hana tsagewar fatar fuska saboda sanyi.