Yadda za a magance matsalolin ganin wata (1)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai.  Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halitta, Annabi da alayensa da sahabbansa.GabatarwaGodiya ta tabbata ga Allah Madaukaki. Muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa, kuma muna neman gafararSa. Kuma muna neman tsarinSa daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar da shi, to […]

Yadda za a magance matsalolin ganin wata (1)
Yadda za a magance matsalolin ganin wata (1)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai.  Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halitta, Annabi da alayensa da sahabbansa.
Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukaki. Muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa, kuma muna neman gafararSa. Kuma muna neman tsarinSa daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar da shi, to babu mai batar da shi. Wanda kuma Allah Ya batar da shi, to babu mai shiryar da shi. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah, kuma na shaida Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam -SAW) bawanSa ne kuma ManzonSa ne.
Bayan haka: Lallai ne ilimin kimiyya yana da babbar gudunmawar da yake bayarwa a fagen da ya shafi al’amarin addini, musamman ta gefen duban wata da kuma neman Alkiblah ko gyaranta, kamar yadda a da ake amfani da irin su taurari da wata da rana da inuwa da sauransu.
 Kodayake har yanzu ba a daina amfani da su ba, tare da haka, kuma yanzu a wannan zamani na na’urar kwamfuta, an samo hanyoyi mabambanta wadanda za a iya amfani da su wajen yin irin wadannan ayyuka. Wanda ya sani, ya sani, wanda kuma bai sani ba, to sai ya yi kokari ya sani, kada ya sake a bar shi a baya.
To da farko dai, ita matsalar ganin jinjirin watan Ramadan, matsala ce mai girma, kuma tana damun al’ummar Musulmi, musamman ma ’yan Najeriya. Za ka ga an wayi gari wadansu sun tashi da azumi yau, wasu kuma sai gobe, kai wasu ma sai jibi ko gata.
To abin tambaya shi ne:
1 – Me ya sa wadannan matsaloli suka yawaita?
2 –  Ko wata zai iya fitowa da safe kuma a gan shi da yamma a matsayin sabon wata?
3 – Me ya sa wata ba ya fitowa, sai bayan kwana biyu ko akalla daya  daga sanarwar  shugabanni?
4 – Me shari’a ta ce idan wata ya tsaya da girma a daren farko?   
5 – Akwai bambancin sabon wata ne a tsakanin shari’a da kimiyya?
6 – Me shari’a ta ce game da shaidu, idan ba a ga wata ba washegarin ranar 30?  
7 – Muna lura da ayoyin Alkur’ani da hadisai da maganganun magabata kuwa?     
8 – Mece ce mafita a cikin wadannan matsaloli?
Insha Allahu, za mu samu amsar wadannan tambayoyi a cikin wannan takaitacce bincike. Allah Ya sa mu dace.
To ga wasu daga cikin amsoshin wadannan tambayoyi a karkashin binciken da na yi, kuma nake so in gabatar da shi, a takaice, ga al’ummar Musulmi, musamman ma shugabanni, domin su ne masu fada-a-ji.
1 – Me ya sa wadannan matsaloli suka yawaita?
Amsa ita ce kamar haka:
 a) – Rashin ilimin masu duban wata, domin shi jinjirin wata ganinsa yana tabbata ne da ganin adalai akalla mutum biyu. Wadanda suka san ilimin, Allah (SWT) Ya ce,  “Duk wanda ya riski (ya ga ko ya ji labarin ganin) watan Ramadan daga cikinku, to ya azumce shi.” (Bakara: aya ta185).
Malamai sun yi fassara daban-daban a kan wannan aya da ke ba da ma’anar riska ko gani ko jin labari, sai dai wacce ta fi fitowa fili ita ce gani da ido, saboda Hadisin Manzon Allah (SAW) da ya ce: “Kada ku dauki azumi, har sai kun ga jinjirin wata, kuma kada ku ajiye (azumi) har sai kun gan shi. Kuma idan ya buya daga ganinku, to ku cika lissafin Sha’aban ya zama kwana talatin.” (Kitabus-Siyam “Tanwirul Hawaliki, 269”, Sharhin Muwadda Malik).
Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kada ku riga Ramadan da azumin yini daya ko biyu.” (Buhari da Muslim da Tirmizi  da Nasa’i ne suka rawaito shi).
b) – Rashin tantancewar da ta dace da masu kawo labarin ganin wata. Hanyar da ake tantance masu ganin wata ita ce: Idan masu duban (ganin) watan, a misali su biyar ne, to, sai a zaunar da su a waje, a kira su daya bayan daya, sai a (rika) yi musu tambayoyi kamar haka:
i – Daga gurbin faduwar rana, wane gefe watan ya tsaya, dama ko hagu?
 ii – Ina watan ya karkata, Kudu ko Arewa ko sama?              
iii – Lokacin da ka ga watan, yaya dagowarsa take zuwa sama?      
ib – Wane lokaci ka gan shi, kuma yaushe ya fadi/ bata?
 To, idan bakinsu ya zo daya, fani’ima, abin nema ya samu; idan kuma suka yi sabani wajen ba da amsa, to akwai matsala ke nan, sai a warware ta ta hanyar da ta dace.
 Dalilin yi musu wadannan tambayoyi kuwa shi ne maganar Allah, Mai girma: “Ya ku wadanda suka yi imani! Idan mai ba da labari ya zo muku da wani labari, to ku nemi bayani (ku yi bincike –ku tantance) domin kada ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci kuma har ku wayi gari kuna masu nadama (da-na-sani) a kan abin da kuka yi,” (Hujrat: ayah ta 6).
c) – Yawaitar karya a wannan zamani. Wani don kawai a ce masa yana cikin wadanda suka ga wata, sai ka ga ya yi karya. Allah Ya sauwaka.
) 2) Ko zai yiwu wata ya fito da safe kuma a gan shi da yamma a matsayin sabo?
Amsa:  Ilimin shari’a da na kimiyya sun tabbatar da cewa baya yiwuwa a ga tsohon wata da safe, sannan a sake ganinsa da maraice a cikin yini guda.
Imam dabari ya ce: “Manzilolin wata 28 ne da kuma kwana biyu  na nukusani (wato idan wata ya cika kwana 30 ke nan.
Allah (SWT) Ya ce, “Rana ba ya kamata a gare ta, ta riski wata.  Kuma dare ba ya kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukansu a cikin sarari guda suke yin iyo”. (Ya Sin: aya ta 40).
Imam Al’aufi ya ce, an karbo daga dan Abbas a kan ma’anar: “Walkamari iza talaaha”, wato “Kuma da wata idan ya biyo ta (ita rana).” (Shams: aya ta 2. Ma’ana, wata yana bin rana.
Ibnu Taimiyya ya ce, “Wata yana buya dare daya, wani lokacin kuma yana buya dare biyu. Kai, har dare uku ma yakan buya.” (Majamu’ul Fatawa, Juzu’i na 25, shafi na 180).
To ka ga ke nan babu yadda za a yi wata ya fito a zangonsa na karshe a matsayin tsohon wata, sannan kuma da yammacin wannan yinin ya sake fitowa a matsayin sabon jinjirin wata.
3- Me ya sa wata ba ya fitowa, sai bayan kwana biyu ko akalla kwana daya, daga sanarwar shugaba?
Amsa: Wannan yana faruwa ne saboda mafi yawan duban wata da ake yi yana faruwa ne kafin wata ya kare. To, haka ne mana! Watan nan fa yana da manziloli (masaukai) kuma kowace manzila (masauki) na da minti 49 tsakaninta da ’yar uwarta, kuma ba za ka iya ganin  wata ba, sai idan wata yana da akalla manzila daya tsakaninsa da rana, a ganin ido.
Usman Mahmoud Kabo
(Ramadan) Abu Abdur-rahman
Research Officer (NSCIA),
08034540120, 08055717124