Yadda za a magance rikice-rikice a Kudancin Kaduna – Shugaban CPP
Alhaji Iliyasu Musa shi ne Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam kuma shugaban kungiyar Hadin kan Al’umma don Tabbatar da Zaman Lafiya (Community Peace Partnership- CPP) da kungiyar Matasan Arewa (AYF) na karamar Hukumar Jama’a, kuma jigo ne kulob din Peace Club.’ A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana wasu daga cikin dalilan da ke yawan haifar […]
Alhaji Iliyasu Musa shi ne Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam kuma shugaban kungiyar Hadin kan Al’umma don Tabbatar da Zaman Lafiya (Community Peace Partnership- CPP) da kungiyar Matasan Arewa (AYF) na karamar Hukumar Jama’a, kuma jigo ne kulob din Peace Club.’ A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana wasu daga cikin dalilan da ke yawan haifar da tashin hankali a Kudancin Kaduna da yadda za a magance su:
Aminiya: Kana cikin kungiyoyin samar da zaman lafiya da damaa Kudancin Jihar Kaduna. Ko wadanne ayyuka kuke gudanarwa?
Alhaji Iliya: To bari mu fara da Peace Club, wadda aikinta shi ne cusa wa kananan yara daga kowane addini da kabila da suka kama daga shekara 13 zuwa 24, akidar kaunar juna da zaman lafiya domin su taso da kishin juna domin dinke barakar da ke ke tasowa. Domin an ce itace tun yana danye ake tankwara shi. Amma zan fi yin magana ne da yawun kungiyar CPP. Duk kungiyoyi da na lissafa kungiyoyi ne masu zaman kansu sai dai kowacce aikinta na tukewa ne a wurin gwamnati. Misali abin da ya faru kwanan baya na rikicin Fulani makiyaya da manoma a yankin Godogodo, a sakamakon shiga tsakani da kungiyar CPP da nake shugabanta ta yi ne ya sa Shugaban karamar Hukumar Jama’a ya tura wa Mai girma Gwamna da maganar shi kuma ya turo Mataimakinsa ya zo muka zauna da makiyaya da manoman wajen.
Aminiya: Yankin Kudancin Kaduna na daya daga cikin wuraren da ake yawan samun tashin hankali, me kuke ganin yake yawan janyo tashe-tashen hankulan, kuma ya za a yi a magance su?
Alhaji Iliya: Gaskiya dalilan suna da dama sai dai mafi girma daga ciki shi ne son zuciya. Ka ga akan yi rigima tsakanin Kirista da Musulmi, akan yi tsakanin kabilu kuma akan yi tsakanin makiyaya da manoma amma duk in ka kewayo za ka ga akwai son zuciya, wanda shi ne ummul-haba’isi, na biyu akwai rauni daga wajen gwamnati na rashin hukunta wadanda ake samu da laifin ta da zaune-tsaye. Abin da ya sa nace haka shi ne, bayan kowane rikici gwamnati kan kashe kudi masu yawa ta kafa kwamiti domin zakulo abin da ya haddasa rikicin amma bayan an mika sakamakon binciken an gano masu laifi, ba za ka sake jin wani abu daga nan ba. Sai na uku akwai matsalar shaye-shaye ga matasa wanda sakamako ne na rashin aikin yi. Su kuma laifinsu yana komawa ne ga masu sayar da kayan maye da an san su da duk inda suke amma sau da yawa idan aka kama su sai ka ga bayan kwana biyu an sako su sun ci gaba da muguwar sana’arsu. Na karshe akwai maganar dan gari da bako ko ’yan kasa da baki. Za ka ga mutum mai shekara 70 wanda kakanninsa ma a wurin aka haife su amma da zarar wani abu ya faru sai ka ji wasu kabilun na cewa ai ku baki ne ba garinku ba ne. To idan har aka ci gaba da wannan ba za a samu zaman lafiya ba, domin idan ka dubi wadanda ake ce musu bakin za ka ga wani babansa ko kakansa na daga cikin wadanda suka habaka arzikin garin da garin baki daya amma saboda son rai sai ka ji ana ce masa wai ba garinsu ba ne, ka ga ai ba a nemi zaman lafiya ba.
Aminiya: A lokacin Gwamna Makarfi ya kirkiro masarautu inda kusan kowace kabila ya ba ta sarautarta saboda magance korafin da wadansu ke yi cewa an danne su ko kuma baki na mulkar ’yan kasa, zuwa yanzu za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu?
Alhaji Iliya: Gaskiya kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, sai ma dai ta bata kwalliyar da kazanta. Rikice-rikice nawa aka yi bayan raba masarautu da aka yi a Kudancin Kaduna? Misali masarautar Jama’a wacce take nan fiye da shekara 200, kafin kacaccala ta da aka yi, masarautun Kagoma da Kaninkon da Godogodo da Fantsuwam da kuma Ninzom da Numana da ke karamar Hukumar Sanga a yanzu, da duk suna dunkule ne a karkashin masarautar Jama’a kuma a lokacin babu fitintinun kan iyaka amma bayan raba masarautun za ka ga ana samun matsalolin kan iyaka tsakanin wannan da wancan.
Sannan rikici mafi muni da ya faru a Kudancin Kaduna shi ne rikicin bayan zaben Shugaban kasa na shekarar 2011. Ka kalli rikicin da kyau, rikici ne na siyasa tsakanin jam’iyyun PDP da CPC. A Arewacin Kaduna da cikin Kaduna za ka ga Musulmi dan PDP ya je ya kone gidan Musulmi dan CPC haka shi ma dan CPC Musulmi zai je ya kone gidan Musulmi dan PDP. Amma da rikicin ya gangaro nan Kudancin Kaduna sai kawai ya canja salo inda Kiristoci suka auka wa Musulmi suka kashe na kashewa suka kona na konawa misali a garin Zonkwa da Matsirga da Madakiya da Gidan Maga da Unguwan Rimi da sauransu inda aka tashi Musulmi har yanzu ba su koma ba. Shin su da sunan wacce jam’iyya aka auka musu? Me ya sa aka ba rikicin rigar addini? Tunda an kacaccala sarautun kowa an ba shi nasa, a garin Zonkwa akwai wani sarki ko dagaci ne Musulmi? To me ya sa aka auka masa? Me ya kawo wannan rigima? Ka ga har yanzu dai bayar da masarautun bai kai ga magance matsalolin da aka guje ba, wannan shi ne son zuciyar da nake fada, son zuciya irin na ’yan siyasa.
Aminiya: Wane kokari kungiyarku ke yi don fadakar da jama’a da gwamnati idan kuka hango wata kura na shirin tashi?
Alhaji Iliya: Wannan kungiya ta CPP, reshe ce na Kwamitin Sulhuntawa na Najeriya ‘Nigeria Reconciliation Committee’ da yake karkashin wata kungiya a Birtaniya wacce da ta hangi irin matsalolin rashin tsaro da rashin zaman lafiya sai ta kuduri niyyar taimakawa don magance su. Da ta shigo sai ta hadu da wata kungiya da ke karkashin cocin Katolika mai suna, wato Debelopment Peace Initiatibe (DPI), su suka hadu suka kafa CPP. Akwai wakilan JNI da CAN da na kungiyoyin mata da na ’yan kasuwa da na kabilu da na sarakuna da jami’an tsaro da ’yan jarida da nakasassu da sauransu. Wadannan su ne suka hadu suka yi CPP. Aikinmu shi ne da zarar mun ga hayaki na tashi, mu yi maza mu kashe hayakin tun kafin ya zama gobara ya cinye wurare. Wannan ne aikin da muke kan yi yanzu haka a yankin Godogodo.
Aminiya: Wadanne matsaloli kuke fuskanta wajen gudanar da ayyukanku?
Alhaji Iliya: Matsalar dai ba ta wuce ta kudi ba. Ita kungiyar DPI, ita ce idan muka rubuta mata abin da muka kashe take turo mana. Amma bayan ita babu wanda yake taimaka mana.