Yadda za a magance sanko

Mutane da yawa ba su son sanko

Yadda za a magance sanko

Sanko

Mutane da dama ba su son sanko. Sanko abu ne da ke bata kyan mutum, inda yake da nasaba da dangin mutum.

Idan akwai mai sanko a dangin mutum, to zai iya fito masa ko ma a haife shi da shi.
Akwai wasu abubuwa da dama da ka iya haifar da sanko, kamar yawan gajiya ko yawan amfani da launin baki a gashi domin rage furfura da sauransu.

A yau na kawo muku hanyoyin da za a bi don magance wannan matsala.

• A samu man ‘castor’ da man kwakwa, a hada su wuri guda. Sai a rika shafawa a fatar kai, a rufe kan da leda na tsawon minti biyar. Yana da kyau a yawaita yin haka don fitowar gashi.

• A yawaita amfani da ruwan ganyen dogon yaro domin yana tsiro da gashi da wuri kuma yana hana fitowar furfura. A tafasa ganyen dogon yaron, idan
ya huce sai a rika wanke kai da ruwansa.

• Shayin na’a’na’a da ruwan ‘aloe vera’ na dauke da sinadaran bitamin A da E da
kuma C.

Don haka suna taimakawa wajen fitowar gashin da ya zube da
wuri. A rika hada shayin na’a’na’a da ruwan ‘aloe vera’ kadan, sannan a rika sha na tsawon mako biyu za a ga canji.

• Cin albasa na taimakawa wajen fitowar gashi. Yana da kyau a yawaita cin danyar albasa kamar guda biyu a rana.

Za a iya yin kwadonta da rama ko da lansir domin saukin ci. Sannan a yawaita jajjaga ta ana shafawa a inda sankon yake, shi ma zai taimaka.

• kwaiduwar kwai da ruwan lemon tsami da kuma man zaitun na taimakawa wajen fitowar gashi da wuri. A same su a hada su waje daya, sai a rika shafawa a fatar kai. Yana da kyau a rika yin wannan kamar sau biyu a mako.

• A samu ‘baking soda’ da kuma man wanke kai, a rika shafawa a sankon.

Yin haka na magance kowace matsalar fata hade da na amosanin kai, sannan kuma yana taimakawa wajen fitowar gashin kai.

• A hada lalle da man kwakwa wuri guda, sannan a shafa a kan sankon, a bar shi tsawon minti 30. Wannnan na taimakawa wajen magance matsalar sankon da rashin fitowar gashi.