Yadda za a magance shigar Fulani harkar garkuwa da mutane
Dalilan labi ko burtali: Ba sabon abu ba ne a ji ana zubar da jini a tsakanin Filani da manoma saboda zargin an cinye musu labi ko burtali ko wuraren kiwo ta hanyar gina gidaje da gonaki. Alhaji Mu’azu Alhaji wani fitaccen dan jarida, kuma dan marigayi Sarkin Shanun Sakkwato Alhaji Alhaji, ya ce mahaifinsa […]
Dalilan labi ko burtali:
Ba sabon abu ba ne a ji ana zubar da jini a tsakanin Filani da manoma saboda zargin an cinye musu labi ko burtali ko wuraren kiwo ta hanyar gina gidaje da gonaki. Alhaji Mu’azu Alhaji wani fitaccen dan jarida, kuma dan marigayi Sarkin Shanun Sakkwato Alhaji Alhaji, ya ce mahaifinsa kuma babban dan Majalisar Sarkin Musulmi Abubakar na Uku ne ke da alhakin ganin an samu zaman lafiya a tsakanin Fulani da makiyaya. Ya ce dalilin haka ya sa mahaifinsa ya zagaya fadin kasar nan tare da fitar da labi-labi ko burtalolin da makiyaya dabbobin ke bi domin yin kiwo da kuma kaura lokacin rani daga Arewa zuwa Kudu musamman zuwa gabar Kogiin Neja da Kwara, kafin su dawo Arewa da damina. Ya ce a baya an fitar da burtali tun daga Sakkwato har zuwa Legas da kuma Maiduguri da Adamawa zuwa Enugu da sauransu. Ya ce ba a bar burtalolin haka ba, sai da aka haka rijiyoyin burtsatse da kwakware, wannan ya sa a wancan lokaci ba yadda za a yi ka ji makiyayi da manomi suna yi wa juna mugun kallo balle har wani ya kai ga zaro makami don yin fito-na-fito.
Rigimar Fulani makiyaya da manoma:
Bincike ya nuna cewa yin handama da babakere da burtalolin da aka kebe wa Fulani makiyaya ne ummul-haba’isin sa Fulani makiyaya suna yin barna ga wadanda suka yi musu kutse a burtalolin don gina gidajen gona na zamani da sauransu. Wannan ya kai ga kowa na daukar makami don kare dukiyarsa. Bayan nan kuma an daina ba Fulani makiyaya damar zama a gona don cin-rani domin kada a ba su karmami.
Hakan ya sa wasu sun rasa dabbobinsu saboda rashin burtali, wasu sun yin kaura zuwa nesa bayan an gwabza fada da biyan diyya bayan an yi musu shari’a, duk hakan sun sa sun rasa dabbobi. Sai kuma satar shanu da ta yi kamari kwarai a baya-bayan nan.
Wani mahauci kuma Sarkin Fawan Barikin Sojoji na Bonny Camp da ke Legas, wanda yake fawa yanzu a rugunin gidajen ’yan majalisa da ke Abuja, Alhaji Isa Sallau Jibrin ya ce tun yana matashi dan shekara 19 yake jin ana satar shanu ga shi yanzu yana da shekara 69. Ya ce ya dace a dauki mataki don magance wannan matsalar.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce Fulani sun fara satar shanu ne da satar shanun manoma Hausawa da sauran kabilu inda suke cewa don me ake yi musu katsalanda a kan hanyar cin abincin Fulani na gadon-gado.
Fulani da masu garkuwa da jama’a:
Daga bisani sai wasu Fulanin suka fara yin fashi da makami sannan suka gawurta suka tsunduma ga satar Fulani da duk wani mai hannu da shuni a Jihar Kogi suna garkuwa da su suna neman kudin fansa, daga nan sai garuruwan Fulani da ke gefen Abuja har ya yadu zuwa sauran sassan kasar nan.
A yanzu haka ana kai farmaki ga ’yan ta’addar da suka hada da Fulani da Hausawa a dajin Kamuku da ke karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna dajin da ya yi iyaka da jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Zamfara ta amfani da jiragen sama, sai kuma dajin Falgore a iyakar Kano da Kaduna da Bauchi.
Bincike ya nuna cewa dalilin yin garkuwa da mutanen shi ne idan sun barayin suka saci shanu suna samun matsalar safara da sayar da su a kasuwa. Sai suka sauya salo inda suka fara yin garkuwa da ’ya’yan masu dukiya da masu shanu, inda duk wanda aka yi garkuwa da da ko ’ya ko matarsa tilas ya kwashi shanunsa da kansa ya kai kasuwa ya sayar ya kai musu kudin.
Alhaji Husaini Ladugga Kachiya kuma Dallatun Ladugga a masauratar Kachiya da ke Jihar Kaduna yana daya daga cikin jami’an kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) ta kasa, ya ce mafita game da rikicin Fulani makiyaya da manoma da kuma satar shanu, ita ce Sarakunan Arewa su samar wa Filani burtali da labin shanu don masu satar mutanen su tuba a zauna lafiya.
barayin zaune:
Dallatun na Ladugga ya ce in bera na da sata to daddawa na da wari, ya ce ba Bafulatani kadai ke yin ta’asar da ake ta yawan zarginsa ba. Ya ce Bafulatani in ya samu bindiga to wa sayar masa? Wa ya koya masa harbawa? Wa yake sayar masa da harsashi? Sannan Bafulatani ba zai iya sanya wa sa igiya ba, sai dai Bahaushe ko wata kabilar, kuma Bahaushe ko wata kabilar ke karbo sa daga daji ya kai kasuwa a birni ya sayar. Sannan mahauta sun koma yanka sa a daji, su binne kai da fata da hanjin, sannan ana sayar musu da bajimi a kan Naira dubu 20, sai su kawo Naira dubu 10, su ce abin da aka sayar ke nan.
Alhaji Hussaini ya ce ba wai yana goyon bayan Fulani ba ne, amma in an ga laifin Bafulatani to a ga na sauran barayin-zaune da ke taya bera buruntu. Ya ce wadannan abubuwa ana iya cewa sun taimaka wajen sa Fulani fara yin garkuwa da mutane.
Yadda Fulani suka fara garkuwa da mutane:
Wani Bafulatani da bai son a fadi sunansa ya ce yin garkuwa da mutane da ake zargin Fulani da yi, ya yiwo asali ne daga Jihar Kogi sannan ya tsallako Abuja. Amma sai labaran siyasa suka shafe na satar Fulani a kauyukan yankin Abuja musamman a garuruwa irinsu Kuje da Abaji da Kwali. Ya ce abin ba zai yi sauki ba har sai ’yan sanda da sauran jami’a tsaro sun zamo mutanen kirki domin hukunta batagari da Miyetti Allah ke kamawa tana kai musu. Amma a ba da belin mutum ba cikin dan lokaci kadan da kama shi.
Majiyar ta kara da cewa suna sanya duk wani dan ta’addar da ke satar shanu ko garkuwa da mutane da suka kama su tuba ta hanyar rantsuwa da Alkur’ani kafin a sake su, sannan shirin yana samun nasara kwarai.
Maganin rigimar Fulani makiyaya da manoma:
Jarman Gombe, kuma tsohon Gwamnan Tsohuwar Jihar Arewa maso Yamma a zamanini mulkin Janar Yakubu Gowon, Kwamishinan ’Yan sanda Alhaji Usman Faruk, (mai ritaya) ya ce yana rubuta wani littafi dangane da yadda za a magance yawan rikice-rikicen da ke aukuwa a tsakanin Fulani makiyaya da manoma. Ya ce ya bayar da kasida a taron kasa da aka gudanar karshen mulkin gwamnatin da ta shude cewa maganin rigimar ita ce: A samar da manyan filayen kiwo ga Fulani don su zauna waje guda, a samar musu da asibitoci da makarantu da dam-dam wadatattu. Ya ce in ba a yi haka ba, to rigimar sai ta wuce na Boko Haram domin za ta haifar da zaman dar-dar da rashin nama da madara da fata domin rashin abin yi yana haifar da tashin hankali.
Bugu da kari, Gwamnatin Tarayya ta ce tana son sayo ciyawa mai yabanya daga kasar wajen domin shukawa don magance rikici a tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
A zamanin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya dakatar da wani shugaban karamar hukuma saboda ya kasa magance rigima a tsakanini Fulani makiyaya da manoma. Ya kuma ce duk wanda aka yi rigima a yankinsa, zai yaba wa aya zaki, wannan ya sa har yanzu ake zaman lafiya a jihar.