Yadda za a magance warin baki
Idan ana kwalliya kada a manta da tsaftar baki wadda duk yadda mutum ya kai ga kyau idan har yana magana kuma ana jin warin bakinsa akwai babbar damuwa. Yana da kyau a kula da yadda ake wanke baki da hakora da kuma harshe. Domin idan daya daga cikin wadannan ababen da kidanya bai wanku […]
Idan ana kwalliya kada a manta da tsaftar baki wadda duk yadda mutum ya kai ga kyau idan har yana magana kuma ana jin warin bakinsa akwai babbar damuwa. Yana da kyau a kula da yadda ake wanke baki da hakora da kuma harshe. Domin idan daya daga cikin wadannan ababen da kidanya bai wanku ba, hakan zai iya haifar da warin baki. Yawan cin tafarnuwa da albasa da kuma shan giya na haifar da warin baki. A yau na kawo muku hanyoyi da za a bi domin magance warin baki.
• Idan ana sanye da hakorin roba ne, yana da kyau a rika wanke su sannan a cire su a baki a lokacin da za a kwanta bacci da dare. Kwanciya da su a baki na haifar da cututtuka da ke sanya warin baki.
• A yawaita shan ruwa sosai; shan ruwa na wanke kowace datti da ke baki. Yana da kyau a rika kurkura bakin da zarar an tashi bacci, domin fitar da kowace dauda da ke cushe a tsakanin hakora.
• Idan an san ana da warin baki, a kasance cikin wanke baki da magogi hade da man goge baki a duk lokacin da aka gama cin abinci domin magance matsalar wari.
• Yawaita amfani da magogin hakora na haifar da cutar warin baki. Don haka, yana da kyau a rika canza magogi bayan watanni biyu zuwa uku, domin samun hakora masu lafiya.
• Kada a manta zuwa ganin likitan hakora, domin ya taimaka wajen wanke hakoran da magunguna domin rage warin baki.
• A yawaita cin kanamfari sosai, cin kanamfari na magance kwayoyin cututtukan da ke haifar da warin baki.
• Yawan cin ‘ya’yan itatuwa kamar su amfuna da lemu da mangoro da abarba da dai makamantansu na rage warin baki.
• A samu garin ‘baking soda’ sannan a kwaba da ruwa sai a rika kurkure bakin da shi, amma kada a hadiye. Za a iya samun ‘baking soda’ a shagunan da ke sayar da kayakin hadin ket.