Yadda za a magance warin gashi
Yawan barin gashi ya yi dauda sosai ma na janyo warin gashi.
Warin gashin ka na daya daga cikin ababen da ke tada wa mata da dama hankali. Sai a ga mace ta yi ado ta fita amma ana jin wari.
Ba wani abu ba ne illa warin da ke tashi daga gashinta. Saboda matsalar fatar na janyo warin gashin kai.
Yawan sanya man gashi na dada warin gashi musamman idan man ya yi yawa a gashin kuma ya hadu da ruwa sai gashi ya fara wari.
Yawan barin gashi ya yi dauda sosai ma na janyo warin gashi.
• Idan za a sayi man wanke gashi (shampoo) a sayi wanda ke dauke da sinadarin sulphur ko zinc ko kuma mai dauke da anti-bacterial.
• Man wanke gashin ka mai dauke da sinadarin silicyl na magance wadannan matsalolin.
• Za a iya amfani da lemun tsami domin magance warin gashin ka. Bayan an wanke gashin da man wanke gashi sai a matse lemun tsami a hada da ruwa sai a yi wa gashin wankin karshe.
• Ruwan tumatiri na magance warin gashin ka. Kafin a wanke gashi da man wanke gashi, a matse ruwan tumatiri sannan sai a shafa a fatar ka. A jira na tsawon minti 10 kafin a wanke da man wanke gashi (shampoo).
• Ana iya hada ruwan ganyen dogon yaro a cikin man wanke gashi sannan a juya su sosai kafin a fara amfani da shi, yin hakan na rage warin gashin ka.
• Za a iya samun man gashin kai da ke dauke da man labender domin samun kanshin gashi a kodayaushe.