Yadda za a murkushe Boko Haram – Janar Babangida

A Najeriya wace irin rawa kake ganin ya kamata tsofaffin shugabannin kasa su rika takawa wajen kawo gyara a fannin shugabanci? Bari in fara da shugabannin Jamhuriyya ta Daya, a gaskiya sun yi namijin kokari bayan samun ’yancin kan kasar nan. Dole mu jinjina wa irin su Nnamdi Azikwe da Sardaunan Sakkwato da Tafawa Balewa […]

Yadda za a murkushe Boko Haram – Janar Babangida

A Najeriya wace irin rawa kake ganin ya kamata tsofaffin shugabannin kasa su rika takawa wajen kawo gyara a fannin shugabanci?

Bari in fara da shugabannin Jamhuriyya ta Daya, a gaskiya sun yi namijin kokari bayan samun ’yancin kan kasar nan. Dole mu jinjina wa irin su Nnamdi Azikwe da Sardaunan Sakkwato da Tafawa Balewa da Obafemi Owolowo da sauransu.

To amma kada ku manta suna cikin kokarinsu ne sai kwatsam aka fara juyin mulki da soja suka yi A 1966, A 1952 ma an samu juyin mulki a kasar Masar. Kuma wannan juyin mulki na kasar Masar ne ya yi ta haifar da wasu juyin mulkin a sauran kasashe har abin ya zama kamar yayi a Afirka. Yau idan ka ji an yi juyin mulki a kasar Ghana, gobe kuma watakila ka ji an yi wani a Najeriya. Don haka sai abin ya yadu a fadin kasashen Yammacin Afirka, aka kama yayinsa.

Wani babban kalubale da kasar nan take fama da shi a yanzu shi ne matsalar tsaro, ko a nan Jihar Neja da kake zaune akwai kauyuka da dama da suke ta samu farmaki daga ’yan bindiga. Ko wannan wani sabon kalubale da ba a san shi ba? 

Ta yiwu a wancan lokacin kana karami, amma ai a lokacin karbar ’yancin kan kasa, mun yi ta samun tashin-tashina daga nan zuwa can a fadin kasar nan. Mun samu bore da  wasu rigigimu koda a Jamhuriyya ta Daya. Amma dai an fi samunsu a lokacin soja sai kuma watakila yanzu da ake siyasa.

Ta yaya kake ganin za a bullo wa matsalar tsaron don magance ta?

Wannan yaki ne wanda kuma tilas sai mun yi nasara a kansa. Nasarar tasa kuma sai ni da kai da kuma kowa da kowa ya sa hannu, walau soja ne kai ko dan sanda, kai kowane dan Najeriya yana da rawar da zai taka wajen cin nasarar wannan yaki.

Amma dai ni ina zaton wannan matsala ba sabuwa ba ce. Don a 1970, bayan an kammala Yakin Basasa an yi ta samun yawaitar fashi da makami da kashe-kashe a Najeriya, amma sai gwamnati ta nuna ba-sani-ba-sabo har ta yi waje da matsalar.

Ka yi mu’amala da mutane da dama a rayuwarka, amma wani abin mamaki game da kai shi ne yadda kake kiran sunan mutum da zarar ka gan shi wato koda ka dauki lokaci ba ka hadu da shi ba. Mene ne sirrin haka?

Lokacin muna kananan hafsoshin soja, wato ina maganar tun wajen 1963 zuwa 1964, wata sara ce a tsakaninmu a karkashina akwai kimani sojoji 35, haka kuma su ma wasu hafsoshin, don haka muna gasar rike sunayen duk sojoji 35 din nan da suke a karkashinmu. Misali ina rike sunansu da na matansu da na coci ko masallacin da suke zuwa kai har ma sunan garuruwansu. Haka nan aka horar da mu, kuma sai abin ya bi jikinmu.

Da dama ana tuna alherin da tsofaffin shugabannin Afirka suka yi ne bayan ba su. Amma ba a haba-haba da su a lokacin da suke raye, me ke kawo wannan?

Wannan abu ne mai wahala. Domin ina ganin watakila a lokacin da suke mulki ba a ganin abin da suke yi. Amma idan lokaci ya ja sai a fara fahimtar irin abubuwan da suka shuka na alheri. Bari in ba ka misali, a lokacin da na kirkiro tsarin kasuwancin bai-daya, sai mutane suka yi masa bahaguwar fahimta. Wannan abu ne da muka yi a 1986 amma ga shi yanzu 2020 ana sake komawa kansa.

A zamaninka ka kirkiro ma’aikatu da dama da hakan ya sa wadansu suka yi ta suka cewa akwai kudi masu yawa a wajen gwamnati amma kuma ba a ga komai a kasa ba. Ta yaya ka samu kwarin kwiwar ci gaba da aiwatar da irin wadancan ma’aikatu?

A zamanina ban yi sa’ar samun hanyoyin samun kudi ba kamar sauran gwamnatocin da suka biyo baya. Domin lokacin muna sayar da gangar mai a Dala 10 ce kacal, ba kamar sauran gwamnatocin da suka biyo baya ba wadanda wadansunsu sun sayar a Dala 100 zuwa Dala 105 zuwa Dala 120 da sauransu.

Don haka watakila abin da wasu gwamnatocin da suka biyo baya suka samu a shekara daya ni su na samu a cikin shekara takwas. Don haka ne ya sanya muka bullo da tsarin kasuwa na bai-daya wanda kuma yanzu har kasar Ingila ma tana amfani da shi.

Ga shi ka kai shekara 78, yaya kake ji da zaman gwauronta?

Ina da ’ya’ya masu jinkai, kuma suna bakin kokarinsu wajen kyautata mini kamar yadda mahaifiyarsu take yi.

A matsayinka na kwararre kuma tsohon janar. Wadanne matakai ya kamata gwamnati ta bi wajen kawo karshen rashin tsaro da ke addabar kasa?

Abin da ya kamata a maida hankali shi ne bayanan sirri. Misali kamar mayakan Boko Haram, muna bukatar bayanan sirri a kan yadda suke kai hare-hare da aikace-aikacensu da shugabancinsu da dabi’unsu sannan su wa suke karantar da su kuma su wa suke ba su horo da sauransu. Ana bukatar bayanai masu yawa kafin a tunkare su. Kada ku manta ba kamar sojoji suke ba, mutane ne kamar kowa kuma ba su da yawa idan muka kwatanta su da sojojinmu. Babban burinsu shi ne su haddasa asarar rayuka sannan su jefa firgici a zukatan mutane.

Burinsu su haddasa tsoro da firgici a tsakanin al’umma, har mutane su ga cewa gwamnati ta kasa ba su tsaron da ya kamata, wannan shi ne babban abin da suka sa a gaba su rika kai harin sari-ka- noke. Gwamnati tana iya kokarin ta ga cewa ta kawo karshen wannan lamari. Sannan ya kamata al’umma su shigo su ba da gudunmawarsu ta hanyar bayar da bayanan sirri na ayyukansu a kan lokaci ga hukumomi.

A lokacin mulkinka, an horar da dakaru na musamman da aka samar don tsaron kasa wanda aka ba su horo a dajin Sambisa. Yanzu dajin ya koma hannun Boko Haram wacce hanya za a bi wajen kawar da su daga dajin?

Ku ’yan Najeriya ne kuka jawo wannan sansanin ya mutu, domin a lokacin kowa yana tsammanin na yi haka ne don in tabbatar da kaina a mulkin Najeriya. Wannan shi ne dalilin da ya jawo sansanin horon ya mutu. Muna taka-tsantsan da yanayin da ’yan Najeriya suke ciki kamar yadda suka cire tsammani, kamar yadda wadansu suka fito da kungiyar tsaro ta Amotakun da Shege-Ka-Fasa da sauransu. Abin da muka lura da shi ke nan muka yi tunanin samar da wata runduna ta musamman mai karfi, duk da ba za ta kai karfin sojoji ba. Amma idan ’yan sanda sun kasa, ka ga kana da wata runduna mai jiran ko-ta-kwana, idan ita ma ta kasa to a nan sai ka shigo da sojoji. Mun yi kokarin kada mu shigo da sojoji cikin sha’anin al’umma na cikin gida.

Wannan dalilin ya sa muka kafa rundunar musamman mai suna National Guards. Kamar yadda kuka sani ’yan Najeriya suka ce ba su yarda ba, wannan mutum yana so ne kawai ya samu hanyar zama a kan mulki dindindin, suka ce na samar da rundunar ce kawai don in yi maganin wadanda za su yi min juyin mulki da dai maganganu masu kama da haka.

Me ya sa aka kebe dajin Sambisa domin ba rundunar horo a wancan lokaci?

A lokacin mun duba cikin fadin kasa inda zai fi dacewa da bayar da wannan horo, a lokacin Gwamnan Borno ya ba mu shawara a kan Sambisa zai fi dacewa da wajen da za a bada wannan horo.

Yaya kake ji yanzu da Boko Haram suka karbe dajin?

Na ji ba dadi da karbe wannan waje. Amma sai dai mutane za su kara gane abin da muka yi a fili dangane da wannan waje. Yanzu da a ce har yanzu dakarunmu suna can suna daukar horo a wajen, zai yi wahala a karbe dajin daga hanunsu. Da har yanzu ana amfani da wannan dajin wajen horar da jami’ai da hakan bai kasance ba.

 A matsayinka na jagoran al’umma yaya kake ganin rundunonin tsaron da yankunan kasar nan suke yunkurin kafawa?

Tsoro. Domin mutane suna bukatar tsaro. Babban aikin kowace gwamnati shi ne ta samar da tsaro da kuma walwalar al’ummarta. Wannan shi ne babban aikin gwamnati. To yanzu abin da suke yi ke nan. Watakila rundunar soja da ta ’yan sanda aiki ya yi musu yawa, suna bukatar a karfafa su domin a taimaka musu.

A lokacin da ake fafutikar samar da rundunar tsaro daga shiyoyin kasa sai ga shi wadansu kuma suna kira ga a sake fasalin kasa. Me kake gani ya jawo haka?

Wannan dabi’a ce ta ’yan Najeriya. Babban abin takaicin ma shi ne yadda masu sharhi suke tattauna irin wannan batu. Magana ta gaskiya ita ce idan ka yi magana a kan Amotekun mutane za su ce wannan wata dama ce wadansu suke son su kafa kasarsu ta Oduduwa, haka zalika idan yankin Kudu maso Gabas suka nemi kafa tasu rundunar za a ce suna kokarin kafa Biyafara. Wannan dabi’a ce ta ’yan Najeriya haka suke gudanar da al’amuransu. Ta haka koda wani abin ci gaba ne a haka zai shiririce.

Me ya ja hankalinka ka shiga aikin soja?

A lokacin Tafawa Balewa yana shugaban gwamnati an turo har makarantunmu aka dauke mu domin shiga makarantar horar da soji domin mu zama daga cikin Rundunar Sojin Najeriya. A lokacin Janar Yakubu Gowon ya zo makarantarmu ta sakandare a lokacin yana matsayin Kyaftin, ya yi mana bayanai na karfafa gwiwa a kan dalilan da ya sa za a dauke mu aikin soja wannan shi ne dalili.  A cikin ajinmu mutum15 duk sun samu damar shiga makarantar horar da sojoji wato Military College a Kaduna.