Yadda za a rage gumin fuska
Aminiya ta duba wasu hanyoyin da ya kamata a bi wajen magance matsalar.
An canfa cewa, kowace mace mai yawan gumin fuska musamman a hanci, masifaffiya ce.
A likitance ‘hyperhidrosis’ shi ne yake sanya yawan gumin fuska: kamar a kan hanci da goshi da saman lebba da wuya da sauransu.
- An kashe ’yan bindiga da dama, an ceto dabbobi sama da 500 a Neja
- Mutumin da ya fara tattaki daga Ingila zuwa Makkah don sauke farali ya isa Turkiyya
Wani za a gan shi yana da yawan gumi ba tare da ya yi wani aiki ba. Akwai abubuwa da dama da suke sa gumin fuska kamar masu ciwon sukari da yawan jiba da hawan jini da bacin rai da sauransu.
Mata wadanda da suke yawan son kwalliya za su tsani gumin fuska domin kuwa yana bata masu kwalliyarsu.
Babu maganin gumin fuska, amma akwai yadda za ki yi domin ki rage shi.
Hanyoyin rage gumin fuska:
• Ki rage cin abinci wanda ya kunshi borkono ko kayan yaji.
• Yawan shan bakin shayi yana janyo gumin fuska, amma za ki iya ma shan ruwa mai yawa don ya taimaka wajen wanke duk maikon jikinki.
• Ki rage yin amfani da man shafawa mai maiko, domin irin wannan mai zai dada maki gumin fuska. Ki nemi marar maiko don shafa wa fuskarki.
• Cin ’ya’yan itatuwa da kuma ganye kamar lansir da alayyahu da sauransu, za su rage gumin fuska.
• Ki samo ruwan ‘vinegar’ sai ki hada da zuma mai kyau wadda ba a hada da sukari ba, sai ki sha sau uku a rana kafin ki ci abinci.
• Za ki iya samo ganyen ‘mistletoe’ ki tafasa shi da ruwa na tsawon minti 15 sai ki sha yana rage gumin fuska.
• Ganyen alkama yana da kyau wajen rage gumin fuska. Ki tafasa shi, sai ki sha ruwansa domin shi ganyen alkama yana kunshe da sinadarin bitamin C da kuma bitamin B-12 wajen rage maiko da kuma gumin fuska.