Yadda za a samu fata mai lafiya
Mata da dama na kaunar samun fata mai lafiya. Idan aka ce fata mai lafiya a nan, ana nufin fata mai laushi da santsi da kuma sheki da sauransu. Sirrin samun irin wannan fata ba wani abu ba ne, illa ana son mutum ya samu lokacin kulawa da kansa, musamman wajen gyaran fata. Yana da […]
Mata da dama na kaunar samun fata mai lafiya. Idan aka ce fata mai lafiya a nan, ana nufin fata mai laushi da santsi da kuma sheki da sauransu. Sirrin samun irin wannan fata ba wani abu ba ne, illa ana son mutum ya samu lokacin kulawa da kansa, musamman wajen gyaran fata. Yana da kyau a rika kulawa da fata tun kafin fitowar su kuraje da kyasfi da marurai da sauransu. Akwai hanyoyi da dama da na kawo muku a yau, wadanda za a bi domin samun fata mai lafiya.
• A samu garin kurkum da man kwa-kwa sai a rika shafawa a jiki a kullum kafin a shiga wanka safe da yamma. Kuma ana son wannan hadin ya tsaya a fata na tsawon mintuna 30 kafin a wanke.
• A samu farin ruwan kwai sannan a hada da ruwan lemun tsami, sai a rika shafawa a fuska domin hana fesowar fitinannun kuraje a fuska. Yana da kyau a shafa wannan hadin safe da yamma.
• Domin samun fata mai sheki a kwana daya, za a iya samun tumatir daya, sai a hada da kofin madara biyu, sannan a shafa a fuska a kwana da shi. A wanke washe gari domin samun sakamako mai ingantarwa.
• Idan ana son magance yawan gumin fuska; a samu ruwan ‘aloe bera’ sannan sai a hada da garin kurkum. A shafa a fuska na tsawon mintuna 20 kafin a wanke. Haka za a rika yi a kullum.
• Za a iya hada ruwan lemun tsami da zuma idan ana son magance tabon da ke yin baki a fuska. A shafa wannan hadin a fuska kamar sau biyu a rana na tsawon mintuna 30 a kullum har sai tabo ya bata.
• A samu madara cokula biyu da ruwan lemun tsami cokula biyu, sannan a hada a shafa a fuska da jiki domin samun fata mai sheki.