Yadda za a samu fatar fuska mai sulbi
Hanyoyi biyar na kawar da kuraje da kuma hana fesowarsu a fuska.
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan fili namu na kwalliya.
Kamar yadda ake cewa “riga-kafi ya fi magani” don haka ne a yau na kawo muku hanyoyi biyar da za a bi domin kare fuska daga fesowar kuraje da wasu cututtuka.
Yana da kyau mace ta fi kulawa da fuskarta fiye da komai a jikinta. Domin, kafin a hango komai a jikinta, fuskar za a fara hangowa.
- Ana iya yi wa fuska tausa.
Kamar yadda kowace gaba a jiki ke son tausa, haka fuska ma tana son ana yawan yi mata tausa kamar sau daya a rana.
Yin tausa ga fuska na taimakawa wajen kara karfin fuska da kuma kare ta daga yankwanewa da wuri a lokacin tsufa.
- A kasance ana yawaita wanke hannu.
Domin hannu na dauke da wasu cututtuka da idanu ba su gani. Ya kamata ana wanke hannu sosai a kullum kafin a wanke fuska da shi ko kuma a shafa mata man fuska.
Idan hannu mai dauda ya hadu da fuska, hakan zai haifar da wasu kwayoyin cuta a fuskar.
- Kafin a shafa wani mai a fuska, yana da kyau a bude ramukan gumi a fata.
Kuma hakan zai yiwu idan ana wanke fuskar da ruwan dumi, ko a saka tawul a ruwan zafi sai a goge fuskar da ita sannan a shafa man.
Yin haka na taimaka wa man fuska aiki sosai ba tare da bata lokaci ba.
- Yana da kyau kafin a wanke fuska a goge ta da magogin fuska.
Yin haka na fitar da matacciyar fata da ta daskare a fuska. Bayan haka sai a wanke ta.
Magogin fuska daban yake da magogin hakori, don haka, za a iya samun magogin fuska a manyan kantunan da suke sayar da kayan kwalliya.
- Sannan kada a sake a yi wasa da cin abinci mai dauke da sinadarin ‘calcium’ kuma a rika shan maganin da zai kara wa kashinmu karfi.
Yawan shan ‘calcium’ zai hana fuska fita daga kamanninta na da koda an tsufa.