Yadda za a samu riba a kiwon kaji – Yalwati
Shugabar Kungiyar Mata Makiyaya Dabbobi da Tsuntsaye ta Jihar Katsina, Malama Yalwati Bature Abdullahi ta bayyana cewa akwai albarka da bangaren kiwon kaji ke da ita muddin an ba su kulawar da ta dace. Shugabar ta ce ta fara kiwon kaji ne tun 1984, inda ta faro daga gidansu, wajen mahaifinta da kaji 10. Ta […]
Shugabar Kungiyar Mata Makiyaya Dabbobi da Tsuntsaye ta Jihar Katsina, Malama Yalwati Bature Abdullahi ta bayyana cewa akwai albarka da bangaren kiwon kaji ke da ita muddin an ba su kulawar da ta dace.
Shugabar ta ce ta fara kiwon kaji ne tun 1984, inda ta faro daga gidansu, wajen mahaifinta da kaji 10. Ta ce cikin ikon Allah duk yanayin da aka shiga ba ta rasa kaji.
Ta ce sukan dauko kajin ne tun daga ranar da aka kyankyashe su daga inji, sai a shirya musu dakin da aka tanada da za a dumama zafinsa daidai da yanayin zafin da ba zai wuce digiri 39 zuwa 40 na celcius ba har zuwa kwana 10. “To a lokacin da aka fara yi musu allurar rigakafi ta farko ana rage musu zafin har zuwa lokacin da gashinsu zai fito ya lullube musu jiki,” inji ta.
Malama Yalwati ta ce, ya danganta da irin kajin da za a sanya, na kwai ko nama, inda ta ce na nama mako biyar an rabu da su. In kuma masu yin kwai ne har sai sun nuna ba su iya ciyar da kansu sannan sai a fitar da su a sayar.
Ta ce ana zagaya kajin akalla sau uku a cikin kowane dare domin ganin halin da suke ciki. “Dalilin yin wannan zagaye da daddare shi ne, akwai yiwuwar zafin da suke bukata ya yi musu kadan, saboda haka za su yi kokarin dunkulewa wuri guda don neman zafi. To duk wadanda ke kasa aka haye su, sai a tarar sun mutu saboda nauyin danginsu. Saboda haka a lokacin rainonsu dole mutum ya zamo shi ne komai gare su. Samun isasshen abinci da magani da kuma tsabtacen wajen da suke domin gudun kamuwa da wata cuta,” inji ta.
Malama Yalwati ta ce, samun kasuwa mai kawo riba cikin lokaci babu kamar kaji. “Babban abin da ya kamata mutum ya fara yi a wajen kasuwancin kaji shi ne, samun abokan ciniki wadanda za ka ba su kaya, su ba ka kudi a kan lokaci. Kajin nama ba su daukar dogon lokaci kamar na kwai. Su kuwa kajin kwai su ne kasuwa mai gudana har na wani lokaci mai tsawo. Ita kazar kwai kafin ta fara ne take cin kudi, amma da zarar ta fara saka kwai, to mutum zai ga kamar kyauta ake ba shi kudin,” inji ta.
Sai dai ta ce, babbar matsalar da ake fuskanta a wajen kajin kwai ita ce, wani lokaci da suke da shi na musamman na kasuwa, ma’ana an fi cinikin kwai a lokutan azumi fiye da kowane lokaci. Sannan in mutum ba ya da tsayayyen abokin ciniki ana samun matsala.
Ta nuna damuwa kan yadda ake samun karancin masu kula da lafiyar dabbobi daga bangaren gwamnati inda ta ce, a da hatta magani sai in babu za a ce a je a saya a waje. “Yanzu ma wani abin shi ne, sai ka je wajen masu sayarwa a waje, kai kana neman Gabas shi kuma sai ya tura ka Yamma. Saboda haka, yanzu babban abin da muke bukata musamman a bangaren kiwon kaji shi ne, likitoci da magunguna. Kajin kuwa a bari mu nemo da kanmu,” inji ta.