Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad
Mun fuskanci ƙalubale a shekarar da ta gabata saboda a lokacin ba ta ɗinka sutura ake ba ta abincin da za a ci ake fama.

Wani matashin tela mai sana’ar ɗinki, Malam Muhammad Sani Tela ya bayyana cewar, ya shafe fiye da shekara 30 yana ɗinki.
Ya ce wannan sana’a ta zama tamkar jini da tsoka a gare shi sakamakon yadda ya riƙe ta da hannu bibbiyu.
- Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC
- An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa
Ya ƙara da cewar, wannan sana’a ta ɗinki sana’a ce da ke da matuƙar albarka idan ka sa juriya a ciki domin kuwa ba sana’a ce da za ka tara kuɗi akai-akai ba nan take.
“Sai dai kuma muddin ka tsayar da gaskiya tare da cika alƙawari to lalle za ka samu babban rufin asirin da baya misaltuwa domin kuwa a kullum in ka fito to kuwa za ka samu abin da za ka yi cefanen gidan ka da sauran buƙatu.
A cewarsa, ya samu fa’ida sosai a wannan sana’a ta ɗinki, domin a cikin ta ya yi aure har ma da ‘ya’ya da sauran kadarori.
“Alhamdulillah, kuma babu abin da ya taimaka min na cimma nasara fiye da jajircewa a kanta.
“Kamar kowace sana’a ita ma sana’ar ɗinki t na da nata irin ƙalubalen domin kamar a shekarar da ta shude sakamakon matsalar rayuwa da al’umma suka samu kansu ciki sai da ta kai ga wannan sana’a ta mu ta samu tasgaro na rashin samun ɗinki.
“Domin lokacin ba ta kayan sawa ake yi ba, jama’a na fafutukar abin da za a ci ne ba’a batun ɗinka sutura.
“Amma a bana lamarin sai godiya domin ya kasance muna ɗinkin sosai idan an kwatanta da shekarun baya.
“Saboda yadda ake samun ɗinki tuni mun rufe karɓar ɗinkin sallah sakamakon al’umma sun fara dawowa hayyacin su saboda sauƙin rayuwa.