Yadda za a sarrafa kirjin kaza

Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na girke-girke. Kirjin kaza ya kasance wani  sashi a jikin kaza wanda akwai nama da dama a wajen. Kasancewar cikowar naman da ke wannan waje ya sanya jama’a da dama ba su cika son wannan gefen kazar ba. Domin ko an yi girki sai […]

Yadda za a sarrafa kirjin kaza

Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na girke-girke. Kirjin kaza ya kasance wani  sashi a jikin kaza wanda akwai nama da dama a wajen. Kasancewar cikowar naman da ke wannan waje ya sanya jama’a da dama ba su cika son wannan gefen kazar ba.

Domin ko an yi girki sai a ji wannan gefen bai cika jin su kayan hadi ba. Kasancewar hakan ne ya sanya a yau na kawo muku yadda za a sarrafa wannan gefen a jikin kaza.

 

Abubuwan da za a bukata

•        Kirjin kaza

•        Fulawa

•        Magi

•        Garin tafarnuwa

•        Garin citta

•        Kayan kanshi

•        Kori

•        Man gyada

•        Kwai

 

Hadi

Bayan an wanke kirjin kazar sosai ta yadda karni zai fita a jikin kazar, sai a samu wuka a yayyanka naman falle-falle kuma da dan tsayi. Sannan a zuba naman a cikin kwano. A bare magi a zuba da garin tafarnuwa da garin citta da kori da kuma kayan kanshi sannan a kwaba su cakuda sosai sannan a samo leda a zuba a ciki tare da hadin sannan a saka a cikin firiji (gidan sanyi) na a kalla tsawon awa daya. Sannan a ciro shi a sake saka shi a cire ledar a zuba a kwano sannan a zuba fulawar a fasa kwai daya a kai a kwaba su sosai.

Bayan haka, sai a dora tukunyar tuya a wuta a zuba man gyada sannan a soya su har sai sun soyu sannan a sauke.

Za a iya cin wannan hadin da bakin shayi ko koren shayi domin samun abin karyawa.

A ci dadi lafiya.