Yadda za a sauya hali zuwa nagartar dabi’a
Kowa na da halinsa, iyaye na fata ‘ya’yansu su zama masu halaye nagari. Amma abin tambaya ta wace hanya ake samun hali nagari? Sai an saurarI mutane, wajen musayar bayanai, domin mutane musamman matasa sun gane magana ba umarni ba ne, dole a fahimtar da mutum ya gane shin gaskiya ne, sai a saki jiki […]
Kowa na da halinsa, iyaye na fata ‘ya’yansu su zama masu halaye nagari. Amma abin tambaya ta wace hanya ake samun hali nagari? Sai an saurarI mutane, wajen musayar bayanai, domin mutane musamman matasa sun gane magana ba umarni ba ne, dole a fahimtar da mutum ya gane shin gaskiya ne, sai a saki jiki da kauyawa.
A daular dabobbi, jinsin mutane sun fi kowace dabba nasara, domin mutane suna sajewa da sabon yanayi. Duk inda mutum ya je zai rayu, sabanin sauran hallitun da Ubangiji ya hallita, wannan ya tabbatar mana da cewa Mahalici ya fifita mutum akan hallitu. Mutum na da baiwar tafiyar da manyan dabbobi!
A hanyar kawo sauyi akan sauya sakon, ta yadda mutanen da ake nufinsu da alheri su rika kokwanto! Abin yi shi ne a shiga mutanen a zauna tare da su a ba su damar bayana ra’ayoyinsu, kar a tilasta masu, idan iyaye ne a bi su a nuna masu hanya ta lumana, sai su bi.
Wai ma mene ne hali? Hali wani abu ne da ake yi, ake gani, yana da ma’auni, ana sauya shi. Hali yana da matakai kamar haka da farko akwai kokwanto, ta hanyar kokwanto ne ake yanke hukunci ko yin zabi. Sai a shirya daukar matsaya, kuma a tsaya kan wannan hanyar har a ga sakamako.
Mutum sai ya dogara da mutum!
Da farko iyaye sun fi kowa tasiri kan halin ‘ya’yansu. Daga bisani kakanni a cikin gida ko abokai, sannan gwamnati kan taka rawar gani wajen halayyar ‘yan kasa! Idan mutane na yin abin da suka ga dama, alama ce ta ba dokoki ko ba a aiwatar da hukunci, idan ana hukunta mabarnata dole a dauki matakin kiyayewa a kowane mataki! A nan ma’aikatar shari’a da alkalai da ‘yan sanda sun shigo a hukumance.
Sauya hali na da muhimmanci wajen tafiyar da al’umma, kuma a nan ake samun canji a siyasance, a tarihin duniya kowane lokaci akan samu canji! Shi yasa wasu kan kalli wasu a matsayin kauyawa, bayan a kauyukansu ko biranensu ana musu kallon wayayyu! Yayin da kuri’a daya na iya kawo canji a tsarin dimokuradiyya!
Canji dole ne, har a kai ga an samu gamsuwa ko kusa da haka, domin duk lokacin da mutane suka samu shugabanni a siyasance. Tabbas sun samu damar tofa albarkaci baka, sannan ga ’yan adawa! Kai kwana dari ma’auni ne a wasu kasashen, ka san idan za ka ci gaba salun-alun. Ba sai an zo zabe ba, idan ka gaza a ma’aikatarka sai ka sauka da kanka, ba cacar baki ba! Ko wannan halayya ita kanka sauyi ce, domin a yau ba wanda zai sauka daga mukaminsa ko takararsa don kansa ko don bai kyautata ba, da zarar an fara haka an samu sauyi.
Wajen sauya hali akan bi wasu matakai daga masu kawo sauyi, sai sun kawo sakon, ko sai ana ganin kimmarsu a al’umma, sannan idan sun yi wani abu, a yi. Akwai na biye da su watau masu saurin fahimta ba sai an hore su ba.
Daga bisani wasu ma kan karbi canjin, musamman ganin ci gaban da wasu suka samu ko saukin da ya samu. Wadannan sune sai sun ga uwar bari, kamar lokacin da ake camfen kan a fito da yara a yi musu riga-kafi sai mutane suka ki kawo ’ya’yansu. Amma da wasu suka gurgunce, sai suka rika kawo su don kansu!
Akwai wadanda ba su karbar canji ko ya aka yi sun narke. Irin wannan narkewa kan sa a rika kallon gayu ko dattijai kamar tsageru ko daskararru. Kuma koyaushe akwai irin wadannan tsagerun watau masu tsatsaurin ra’ayi!
Wani abu da yake da tasiri wajen sauyi shi ne zamani. Yayin sabon abu ko sabon salo! Sabon salo kan zama shigo da wani abu unguwarku, kauyenku ko birninku wanda ba a sani ba, kamar wanda ake gani yake wanke hannun kafin ya ci abinci da bayan ya ci, haka idan ya shiga kewaye sai ya shafa sabulu ya wanke yatsunsa, sai mutane suka fara irin wannan salon don a ce su ma ’yan birni ne, sun waye!
Ko ka samu cikakkiyar kulawa ba shi ba ne zai tabbatar ma da cewa ka tsira daga kamuwa daga cututtuka! Sai dai hakan zai rage wa mutum barazanar kamuwa da cututtuka. Mafi yawancin abubuwan da likitoci suke fada mana, fa’idoji ne gare mu, da al’umma baki daya!
Wani kan yi tunanin me zai hana ya ba dansa ruwa, musamaman ana zafi! Maganar zahiri jarirai ba su bukatar ruwa, ba ruwan Zam-zam ba ne illar! Bututun da famfunan da robobin da Zam-zam kan shigo kafin ya zo kofar gidanka na dauke da dauda, ’yan kwallo wani sa’in ma guba!
Wajen sauya hali an gane cewa idan mutum bai ci ya koshi ba a lokacin yana jariri, akwai yiwuwar ya kamu da olsa, haka yana iya fama da barazanar kamuwa da ciwon suga, mutuwar barin jiki, hawan jini, cutar daji da sauransu.
Mata suna da tasiri kan mazaje, wani abin sai an bi ta jakadiya. Haka kakanni da masu unguwa, ko ma in ce sarakuna na da muhimmanci wajen kawo canji, sannan sau da yawa malamai watau limamai ko ladanai su kansu sun isa wajen shiga gaba don kawo sauyi. Domin mutane, musamman talakawa kan yi imani da abin da malamai suka fada, saboda haka a kan so a bi ta hanyar malamai wajen isar da sako. A haka ma gayu kan zama wakilan canji, domin sun fi jan hankalin matasa, da manyan gobe.
Wajen sauya wa mutane dabi’unsu sai an bi a hankali domin wasu mutanen kamar macizai suke da zarar ba su fahimci inda aka dosa ba, ko ba a toshe bakinsu ba, sai su watsa guba ga sakon, a bisa haka sai an yi maganin jita-jita! Kuma yana da muhimmanci a takaita bayanai, a yi magana kan maudu’i daya, kar a rika shiga nan ana fadawa can, sai a rikita mai saurare.
Sauya sako na da muhimmanci fiye da yadda ake zato domin wayar da kai, mutane kalilan sai su fadakar da ’yan uwansu, daga nan masu rinjaye su fahimtar da sauran, domin mutanenmu a kwarya suke, koya ka yi ba za su fahimta ba sai ka yi da gaske, za ka ga mutum yana sa kaya kamar dan birni amma kifin rijiya ne!
A kan bi matakan kafofin yada labarai wajen tallata sako ga jama’a, wani lokaci masu shela ma sun wadatar. Shi ya sa yana da kyau a rika karanta jaridu da mujallu ko sauraren radiyo, watau samun labarai ta kowace hanya, domin ko Allah ya kiyaye aka ce, ya wadatar. Haka ke tabbatar da cewa sakon ya isa, kuma an sauya hali!
Buhari Daure [email protected], Modoji, Katsina.