Yadda za a sauya salon yakar matsalar tsaro a Arewa

Sabbin hanyoyin da za a bi tunda na gwamnati ba su biya bukata ba

Yadda za a sauya salon yakar matsalar tsaro a Arewa

Me ya sa matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a yankin Arewa maaso Yamma? Wane tasiri yakin da dakarun musamman suke yi a yankin ya yi kawo yanzu?

Wadannan tambayoyin sun bijiro ne sakamakon karuwar labarun garkuwa da mutane da hare-haren ’yan bindiga da kuma tilasta wa manoma biyan haraji a yankin.

Tabarbarewar tsaro a Arewa maso Yamma babbar alama ce ta yadda harkar tsaron Najeriya ta sukurkuce.

Gaza magance matsalar da dakarun da aka jibje a yankin suka yi da kuma halin ni-’yasu da ayyukan’yan bindiga suka jefa al’ummar yankin abubuwa ne a fili.

Wata tambayar ita ce; a bisa wane dalili talakawan da gwamnati ke karbar haraji daga hannayensu don biya da inganta rayuwar jami’an tsaro za a bar su a igiyar ruwa ta yadda ’yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka tare da azabtar da su?

Sanin kowa ne cewa talakawa sun cika nasu bangare na yarjejeniyarsu da masu mulki ta hanyar zaben su da suka yi.

A wani lokaci ma sukan ba jami’an tsaro hadin kai tare da samar masu da da bayanan sirri game yiyuwar kawo hari ko take-taken miyagun mutane.

Muhimmin alhakin da ya rataya a kan gwamnata ga talakawa shi ne kiyayewa da kuma ba da tsaro ga rayuka da kuma dukiyoyinsu. Sannan kuma ta sama masu ababen more rayuwa.

Kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Kasa na 1999 ya takaisu ya kira su da “Bada da tsaro da kuma ci gaban jama’a”. wanda kuma a takaice ake wa lakabi da ‘’Muhimmin aikin da ya rataya a wuyan gwamnati.”

Shin gwamnatin ta cika wannan muhimmin bangare na alkawarinta da jama’ar Najeriyar?

A watannin baya an hakaito gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari yana cewa “Ba zan iya hada idanu da talakawa ba saboda mun kasa wajen samar masu da tsaro kamar yadda muka yi rantsuwar ba da kariya ga rayukansu da dukiyarsu.”

’Yan Najeriya da dama sun nuna damuwarsu game da yadda harkar tsaro ta tabarbare a Arewa maso Yamma.

Haka kuma sun bayar da shawarwarin hanyoyin da za a bullo wa lamarin wadanda ba tilas na amfani da karfi ba ne don ganin an maido da dawwamammen zaman lafiya a yanki baki daya.

Sun kuma yi karin haske kan yadda gwamnati za ta dauki matakai da sabon salo wanda zai kunshi sa hannu da kuma gudunmuwar dukkannin masu ruwa da tsaki don kawo sauyi da zai samar da zama lafiya.

Yadda za a yaki ’yan bindiga -Sheikh Gumi

Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana cewa yin sasanci da ’yanbindiga ba zai sanya a samu tsaro ba a yankin.

Ya ci gaba da cewa “ Za a iya amfani da hanyar da’awa. Amma idan kana maganar a yi sulhu ne da Fulani ’yan bindiga sai in ce maka wannan ba mai yiwuwa ba ne.

“Domin su masu laifi ne da ba su da wani tsari a kan kansu. Ka ga za ka iya sasanci da ’yan ta’adda kamar na Boko Haram saboda su suna da dan tsari.

“Su idan suka ji wuta za ka iya zama da su ku yi yarjejeniyar tsagaita wuta.

“Amma in kana maganar yadda za a kauda ’yan bindiga ne a wannan sashe to sai in ce maka za a iya haka ne kawai ta hanyar dibar wasu matasa daga cikin su Fulanin a ba su horo da makamai su koma dajin su yake su da kansu.”

Shehin malamin ya ci gaba da cewa “Kwanakin baya wasu Fulani sun kawo mini ziyara daga Kachia kuma suka yi mini korafi a kan yadda ’yan bindigar suka dame su sun hana su noma.

“Sai na tambaye su shin su ’yan bindigar nan da suke a cikinsu sun kai su nawa? Sai suka ce za su kai kamar 1,000.

“Sai n ace ku kuma kun kai ku nawa a wajen sai suka ce sun kai su 50,000, sai na ce musu shin kuna jin idan aka dauki matasa 3000 daga cikinku aka ba su horo da kayan aiki ba za u iya yin maganinsu ba?

“Sai suka ce mini ai gida-gida ma za su iya bin su su kakkama su.”

Tattaunawa da maharan Zamfara

Wani mazaunnin garin Dansadau ta Jihar Zamfara da baya son a ambaci sunansa ya bayyana cewa za a iya ganin bayan matsalar tsaro a yankin ta hanyar tattaunawa da Fulani masu kai hare-hare.

Mutumin ya ce “Idan da za a iya samar da wani kwamintin zaman lafiya wanda ’yan bindigar da kuma jama’ar gari suka aminta da shi, to za a iya tattaunawar da za ta iya dawo da zaman lafiya.

“Ya kamata ne kwamitin ya samu shugabancin manyan sarakuna da manyan malamai da Ardo-ardo da kuma shugabannin kungiyoyin Fulani da na jami’an tsaro da kuma dattawa da manyan mutane daga wannan sashe da ba ’yan siyasa ba.”

Audu Sada, wani matashi ne wanda ya rasa mahaifinsa da ’yan uwansa shida a wani hari da ’yan bindiga suka kai cikin watan Afirilun 2020 a kauyen Gurzar-Kuka na Karamar Hukumar Danmusa, Jihar Katsina.

Matashin ya bayyana wa Aminiya cewa, “A lokacin da ’yan bindiga suka kawo mana hari mahaifina bai gudu ba.

“Tsayawa ya yi ya fafata da su a kokarinsa na kare iyalansa kuma a haka ya yi shahada tare da ’yan uwana shida.”

Toshe hanyoyin samun makamai

Audu ya bayar da shawara a kan yadda za a kawo karshen ta’addanci da cewa “Za a iya kawo karshen ’yan bindiga ne kawai idan gwamnati ta gano tare da toshe hanyar da suke samu makamai.

“Daga nan kuma sai a nemi hadin kan sarakunan gargajiya, musamman hakimai zuwa kan Ardo, domin su ne suka san duk Fulanin da ke zaune a yankunansu kuma sun san na kirki sun san na banza.”

Adalci ga kowane bangare

Sakataren Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na Kasa, Alhaji Uthman Baba Ngelzama a cikin hirarsa da Aminiya ya bayyana cewa idan har ana son a samar da zama lafiya a yankin Arewa maso Yamma to sai gwamnati ta yi wa kowane bangare adalci.

Domin a cewarsa, al’ummar Fulani su suka fi kowa cutuwa a halin da ake ciki na rashin tsaro yanzu a Najeriya.

“Abubuwan da suka kai mu ga halin da ake ciki a yanzu na rashin tsaro suna da dama.

“Da farko da akwai maganar rikicin makiyaya da manoma wanda dadadden abu ne.

“Sai matsalar wuraren kiwon gandun da matsalar madatsun ruwa da matsalar sha da fataucin kwayoyi da matsalar shigar makamai hannun fararen hula da kuma matsalar burtali.

“Dukkanin wadannan matsaloli babu wacce gwamnati ta mayar da hankali a kanta har ya zuwa lokacin da abubuwa suka dagule.

“Don haka idan ha rana son dawo da zaman lafiya sai an tsaya an magance wadannan matsaloli.

“Hakan kuma bai yiwuwa har sai an kafa Ma’aikatar Raya Harkokin Fulani kamar yadda aka kafa ta Neja-Delta,” inji Ngelzama.

Fulani sun fi kowa cututuwa

Ya ci gaba da cewa “Fulani sun fi kowa cutuwa a halin da ake ciki a yanzu domin ana sace su ko a sace dabbobinsu a daji ba wanda ma ya ji labarin.

“Ka dauki misalin Bafulanin da zai kwanta barci yana da shanu kamar 200 amma garin Allah ya waye ya tashi ba shi da ko saniya. An kore!

“Kuma idan ya kai kara gaban ’yan sanda su rufe shi a bayan kanta su ce sai an yi belin shi.

“Kai koda ma Fulanin da ake kamawa da laifin satar mutane ai za ka gane cewa akwai masu yin amfani da jahilcinsu.

“Domin za ka ji sun karbi kamar miliyan 10 kudin fansa amma ya ce shi watakila 20,000 kawai aka bashi a ciki kuma bai san wadanda ma suke karbar manyan kudin ba.”

An mayar da Fulani saniyar ware

Alhaji Usman ya kuma yi zargin cewa dukkanin tallafin da gwamnati take bayarwa a wuraren da aka samu tashin hankali ba a baiwa Fulani.

“Ko a wuraren da ake samun tashin hankali za ka iske ba a bai wa Fulani tallafin gwamnati; ko da tsugunar da su ma ba a yi.

“Kai ko a tsare-tsaren tallafin gwamnati na rage fatara babu Fulani a ciki; Kuma ina kalubalantar duk wata hukuma ta gwamnati da ta musa hakan ta zo ta kawo mana inda suka sanya Fulani a cikin tsare-tsaren tallafinsu.”

Hanyoyin inganta tsaro

Da yake Karin haske a kan hanyoyin inganta tsaro, Ngelzama cewa ya yi “Ka ga maganar tsarin zaunar da Fulani waje daya a koya masu kiwon zamani abu ne mai kyau, domin ko ba komai za su samu damar ba wa ’ya’yansu ilimin zamani.

“To sai dai ba a dauke shi da muhimmanci ba domin kama daga Gwamnatin Tarayya har na jihohin duk zancen a takarda kawai yake.

“Ya dace dukkannin jihohi sun maido da biyan jangali kamar yadda Jihar Adamawa ta maido da shi.

“Domin ta haka ne sarakuna za su san makiyan da suke zaune a yankunansu da kuma yawan dabbobinsu.

“Ka ga ta haka za su san na kirki da na banza, haka kuma idan bako ya sauka za su sani walau na kir ne ko na banza.”

‘Babu asara a samar da tsaro’

Sanata Ireogbu masani ne a kan harkar tsaro wanda ya ce duk wani kokari da gwamnati za ta yi don kawo zaman lafiya a Arewa maso Yamma ba asara ba ne.

Ya ce babu wata hanya guda daya da za ta iya maido da zaman lafiya a yankin.

Sanatan ya ce, “Kuskuren shi ne a yi tunanin cewa akwai hanyar daya mai iya dawo da zaman lafiya.

“Amma maganar a kafa kwamitin samar da zaman lafiya da ya kunshi sarakuna da malamai da shugabannin Fulani da jami’an tsaro a karkashin jagorancin gwamnatin tarayya abu ne muhimmi, domin ita gwamnati ita ce gaba da kowa.”

Ireogbu ya ci gaba da cewa “Matsalar ’yan bindiga ta fara ne kadan.

“Kafin ka ce kwabo kuma ’yan ina-da-yaki da kungiyoyin ta’adda na ISWAP da wasu na yankin Sahel da kuma masu safarar makamai suka amshe ragamarta.

“Don haka lokaci ya yi da gwamnati ya kamata ta fara gadin kan iyakokin kasar nan ta amfani da jirage marasa matuki da kuma wasu fasahohi na zamani.”

Daga karshe kuma ya nemi gwamnati da ta kara kaimi wajen samar wa matasa aikin yi tare da ba wa sarakuna muhimmanci saboda su ne suka san tarihin matsalolin da kuma hanyoyin warware su.

Anya kwamitin zaman lafiya mifata ce?

Shi kuma Shugaban Kungiyar Fulani ta GAN Allah na kasa, Alhaji Sale Bayari ya nuna shakkunsa wajen yiyuwar samar da zaman lafiya ta hanyar kafa kwamitin samar da zaman lafiya.

Ya yi zargin cewa wasu kungiyoyin Fulani tuni sun nuna kasancewarsu baragurbi ta hanyar alakanta kansu da ’yan bindiga.

Bayari ya ce “Idan har ta tabbata akwai kungiyoyin Fulani da suka karbi kudi daga Gwamnatin Jihar Katsina suka kai wa ’yan bindigar da suka sace dalibai 344 daga makaranta a garin Kankara, to kuwa wannan na nuna cewa sun riga sun bayar da al’ummar Fulani kuma sun bata mana suna.

“Don haka zai yi wuya ka dauki irin wadannan mutane ka sanya su cikin wani kwamiti da sunan kawo zama lafiya.”

Zaman tattaunawa da bangarori

Sheikh Dokta Nuraini Ashafa wanda shi ne Shugaban Kungiyar Kawo Zama Lafiya da Fahimtar Juna Tsakanin Musulmi da Kirista da ke Jihar Kaduna, a hirarsa da Aminiya ya bayyana cewa dama idan ruwa ya yi tsami sai akuya mai geme.

Saboda haka tattaunawa ita ce kadai hanyar da a yanzu ya kamata a bi don sake dawo da zaman lafiya a yankin.

Sheikh Ashafa ya ce, “Abin da ya sa ka ga tattaunawar da aka yi da ’yan bindiga ba ta dore ba shi ne saboda an sanya siyasa a ciki.

Amma idan da za a kafa kwamitin zaman lafiya da ya kunshi malamai da sarakuna da shugabannin Fulani da jami’an tsaro to kuwa za a cimma nasara.

“Domin irin haka ne muka yi a kasar Kenya a tsakanin al’ummar Kalenji wadanda makiyaya ne da kuma na Kikuyu kuma aka samu nasarar dawo da zaman lafiya a tsakaninsu.”

Muhimmancin sarakuna

Da yake tsokacinsa Dan Majen Daura, Alhaji Kabiru ya bayyana cewa za a iya dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma idan aka samar da kwamitin zaman lafiya.

Dan majen ya ce “Mun tsinci kanmu a cikin wannan hali da muke a yau saboda masu rike da madafun iko sun daina sauraron shawarar sarakunan gargajiya.

“Su kuwa sarakunan su ne suka san jama’arsu da kuma matsalolin da suke fuskanta da kuma yadda za a magance su. Don haka idan ana son dawo da zaman lafiya sai an koma an sake lale an mayar wa sarakuna ikonsu.”

 

Shugaban Kungiyar Kawo Zaman Lafiya ta Yankin Masarautar Atyap da ke Zangon-Kataf a Kudancin Kaduna, Mista John Bala ya bayyana cewa ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna ne kawai za a iya samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Arewa maso Yamma.

Mista John ya ce, “ Mun samu nasarar maido da zaman lafiya tsakanin Fulani da wasu al’ummomin Zangon-Kataf ta hanyar tuntubar juna mu tattauna matsalolinmu.

Duk da yake akwai masu yi mana tirjiya daga farko, amma daga baya sun fahimci muhimmancin zama lafiya da juna.

Don haka ina ganin ta irin wannan hanya za a iya maido da zama lafiya a yankin Arewa maso Yamma.”

An shafe shekaru ba tare da hanyoyin da gwamnati ke bi na yaki da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro sun  kawo karshen matsalar da ta addabi yankin ba.

Lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta daina ba da uzurori marasa karfi ta saurari shawarwarin jama’a ta dauki matakan da suka dace don maganin wannan matsala ta ’yan bindiga da masu satar mutane.

Wani rahoton da Aljazeera ta ruwaito dai ya nuna cewa a cikin shekaru tara ’yan bindiga sun kashe fiye da mutum 8,000 tare da tilasta wa wasu 200,000 yin hijira daga wuraren zamansu.