Yadda za a shawo kan matsalolin Nijeriya — Sarki Sanusi II
Ina da yaƙinin cewa al’ummar ƙasa baki ɗaya na fuskantar ƙalubalen da aka gada.
Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya na fuskantar ƙalubale wanda ta gada.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin jami’an gwamnatin jihar Kano da suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa ta Gidan Dabo a ranar Alhamis.
- JAMB ta bankaɗo ɗalibai 3,000 da suka kammala digirin bogi
- An naɗa mace ta farko shugabar sojojin Kanada
Sanusi ya ce, al’ummar ƙasar ba za su ci gaba da kokawa kan ƙalubalen da ake fuskanta ba, yana mai jaddada cewa yana da yaƙinin cewa za a iya shawo kan ƙalubalen ta hanyar juriya da halin da ake ciki.
“Ina da yaƙinin cewa al’ummar ƙasa baki ɗaya na fuskantar ƙalubalen da aka gada, jihohin ma suna fuskantar ƙalubalen da aka gada, amma mafita ba ita ce a riƙa kukan abin da ya faru a baya ba, ba za mu iya ci gaba da kukan ba, ba tare yin komai a kai ba.”
“Ina da yaƙinin cewa mutanen Kano tare da gami da dogon tarihinmu na tsayin daka kan kyawawan halaye za su iya shawo kan waɗannan ƙalubale.
“Yana da kyau a bai wa jama’a shugabancin da zai tsara su kuma su san cewa za su iya tsayawa da ƙafafunsu ba wai su yi ƙasa a gwiwa ba,” in ji shi.
Yayin da yake yaba wa gwamnatin jihar kan manufofinta na ilimi da fansho da kuma biyan kuɗin alawus-alawus, Sarkin ya kuma shaida wa jami’an cewa kowace irin shawara da tuntuɓa ƙofofinsa a buɗe suke.
Ya ƙara da cewa masarautar za ta ci gaba da yi wa gwamnatin jihar addu’ar samun nasara.
Tun da farko Kwamishinan Yaɗa labarai na jihar, Malam Baba Halilu Dantiye ya shaida wa sarkin cewa, jami’an sun ziyarci fadar ne domin nuna wa masarautar irin nasarorin da gwamnatin Kano ta samu a ƙarƙashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf cikin shekara guda.
Ya kuma ce sun kai ziyarar ne domin neman gudunmawar sarkin wajen ciyar da jihar gaba.