Yadda za a shawo kan rikicin kabilanci da addini

Najeriya cike take da abin mamaki idon har kana bibiyar al’amurran yau da kullum,  domin Najeriya ce kasa kwaya daya tilo wadda aka fi samun rikice-rikice tsakanin al’umma mabambanta, duk lokacin da wata hatsaniya za ta barke in har za ka bincika za ka ga tsakanin al’umma mabambantan addinai da kabilanci ke tashi, duba da […]

Yadda za a shawo kan rikicin kabilanci da addini

Najeriya cike take da abin mamaki idon har kana bibiyar al’amurran yau da kullum,  domin Najeriya ce kasa kwaya daya tilo wadda aka fi samun rikice-rikice tsakanin al’umma mabambanta, duk lokacin da wata hatsaniya za ta barke in har za ka bincika za ka ga tsakanin al’umma mabambantan addinai da kabilanci ke tashi, duba da irin yadda malamai suke tashi tsaye tsayin daka wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a cikin kasa, amma duk da hakan abin yakan ci tura, inda ake yawan samun rashin jituwa a duk lokacin da wani abu ya tashi, akan samu munanan tashe-tashen hankula, wadnda kan yi sanadiyar asarar rayuka  da dukiyoyi da samun jikata, a tsakanin wadanda rikicin ya tashi a tsakaninsu. Kai wani lokacin  abin ma yakan shafi wanda bai ji ba, bai gani ba. 

Rikicin kabilanci wani babban kalubale ne wanda ya zama ruwan dare a Najeriya, wanda ya kamata tun daga kan masu unguwanni da sarakunan gargajiya na kowane bangare da ’an majalisun jihohi da shugabannin kananan hukumomi da ’an majalisun tarayya tare da sanatocinmu na kowane bangare da gwamnonin kowane yanki, tareadi da jami’an tsaro, su hadu waje daya domin ganin an magance wannan matsalar gaba daya a cikin wannan kasa,

Saboda batun na zaman lafiya ne, to ya shafi kowa da kowa, domin ana son samun gudunmuwa ta kowane bangare  don a gudu tare a tsira tare, kamar yadda ake fada Najeriya kasa daya uwa daya uba daya al’umma daya in ji wani mawaki, amma dai gaskiya mu ba mu ga alamar hakan ba.

Domin kuwa babu wata ƙasar da za ta ci gaba a duniya face an samu hadin kan ’an kasa  wajen samun yalwatacen zaman lafiya ta kowane fanni.  Kasancewar zaman lafiya shi ne babban abin da duk wani dan kasa yake so, saboda  sai ansamu zaman lafiya sannan arziki zai sallamo a cikin kasa, kowa ya wadata   har wata ƙasa tayi sha’awar shigowa a ciki domin taruwa waje daya a habaka arzikin kasa, 

Bisa la’akari da irin yadda wadanda suka riki Najeriya tun farko kan irin gudunmuwar da suka bayar dari bisa dari, suka tsayu suka tsayu wajen sadaukar da  rayuwarsu da lokacin su, domin kawai ganin kasar nan ta kai a duk inda ake so, kuma sun yi hakan ne ba don tara abin duniya ba, a’a sai dai kawai domin ganin ta zama kasa daya mai cin gashin kanta, har suka bar duniyar nan ba su tara wani abin a zo a gani ba ta gefen tara abin duniyar da za su amfana da shi ko ‘ya’yansu.  

Shin me ya sa mu ba za mu ba da tamu gudunmuwar ba domin ganin ta ci gaba da kasancewa kasa daya mai cikakken Ikon fada aji a duk fadin Africa? Kasancewar Najeriyar ita ce uwa ga Afirka.

Rikici tsakanin Fulani da makiyaya rikici tsakanin addinai da kabilanci. Muke nan, shin ba za mu hada kanmu ba domin samun dimbin arzikin da Allah ya wadata mu da su? Babban abin la’akari a nan shi ne yadda wasu manyan shugabanni suka zuba ido ana ta tafka ta’asa, babu tsawata wa.

Da wannan muke kira da babbar murya ga shugabannin kasa da wadanda alhakin tsawatarwa ya rataya a wuyansu da su yi duk mai yiwuwa domin ganin komai ya daidai a, an ci gaba da samun zaman lafiya mai ma’ana ta kowane fanni,

Kuma muna kira ga ’an Najeriya kwata! da mu hadu domin gina wannan kasa tamu mai albarka. Domin mu gudu tare, mu tsira tare. Allah ka taimaki Najeriya da zaman lafiya da arziki madawwami, da yankin Afirka gaba daya,

Mai Apple Gusau dan kungiyar Muryar Talaka ta kasa reshen Jihar Zamfara.     08133376020/08086679022