Yadda za a shawo kan yajin aikin Malaman Jami’a

A kwananan kusan kowace jarida ko mujalla ka karanta sai ka ga an yi sharhi ko tsokaci kan yajin aikin jami’o’i da aka wuce kwanaki 100 dalibai na gida, ba tare da sanin ranar da za a bude makarantun ba! Haka yasa dalibai ke zaman kashe wando a gidaje, inda wasu suke koyon wasu sana’o’i […]

Yadda za a shawo kan yajin aikin Malaman Jami’a

A kwananan kusan kowace jarida ko mujalla ka karanta sai ka ga an yi sharhi ko tsokaci kan yajin aikin jami’o’i da aka wuce kwanaki 100 dalibai na gida, ba tare da sanin ranar da za a bude makarantun ba! Haka yasa dalibai ke zaman kashe wando a gidaje, inda wasu suke koyon wasu sana’o’i ko kuma aiki domin tafiyar da rayuwarsu, wasu na barci, kuma wannan zaman banzan yasa wasu suke shiga halayen banza kamar karuwanci, kai har ma da ta’addanci wannan halin zai iya haifarwa!
Wannan yajin aikin ya samo asali ne daga saba yarjejeniyar da aka yi da gwamnati a 2009, inda malaman a karkashin kungiyarsu (ASUU) ta gaji da jira! Domin a Najeriya akan ci idan baka yi da gaske ba, za ka jira gawan shanu!
Kowa na da nasa laifi idan muka kalli jami’o’i a halin yanzu ya kamata a ce sun fara dogara da kansu, ba wai kullun su so suke gwamnati ta dauki nauyin komai ba, bugu da kari yadda manyan ma’aikata da farfesoshi suke sama da fadi da dukiyoyin dalibai, duk da ba a fito da abin fili ba, miliyoyi nawa ake badawa gudumuwa daga wajen attajirai, bankuna da kasahen waje? Kudin da ake samu wajen sayar da fom lokacin daukar dalibai? Kudin da dalibai ke biya na rajista da jarrabawa?
Amma abin kunya ko dakin karatu na kirki babu a duk jami’o’in kasar nan, balle madabba’a, ko fanonin da ake da damar amfani da sashen wajen samun kudin shiga kamar bangaren gonaki, idan muka lura da noma da kiwo, kai ko ruwa ne jami’a ta sarrafa sai an samu kudin shiga, ko littattafai da jaridu ne jami’a ta buga sai an samu, amma su kullum a ba su, sai ka ce kishi suke yi da ‘yan siyasa, idan ma haka ne to su tsaya takara a jihohinsu mana in sun yi abin kirki ai zasu sami damar wakiltar kasar!
Amma ko jami’ar Abuja mutum ya je duk da cewa Abuja cike take da gidaje masu alfarma da gine-gine na a zo a gani, amma jami’ar Abuja yadda ka san wata bukka haka aka bar ta. Yana da wuya mutum ya yarda wai jami’a ce! Duk da kudin da ake kashewa wai don su koma mazaunin dindindin amma abin ya ci tura!
Idan da gaske ake ana son gyara harkar ilimi a kasar nan ya zama wajibi ga ‘yan majalisa su sa doka tare da aiki da ita watau dokar da za ta tabbatar da cewa dan kowane ma’aikacin gwamnati da mai rike da mukaman siyasa suna karatu a makarantun gwamnati a nan gida ! Da haka ne ta yaya za a yi watanni uku ana yajin aiki ba tare da sanin ranar komawa ba!
Kai idan harkar ilimi ce ta dame malaman jami’a me zai hana a gyara tsari karatun firamare da sekandere, domin sun fi jami’o’in ma bukatar gyara, duk da babatun da wasu gwamnoni suke wai suna gine-gine!  Idan ka je wasu makarntun firamare sai ka yi kamar ka yi kuka, domin ko karnuka ba za a aje a dakunan da ake kira aji ba! Ta ya za a sami
manyan gobe masu nagarta? Su kansu malaman jami’o’in ‘ya’yansu ba a makarantu ko jami’o’in gwamnati suke ba! ‘Ya’yan malamai sun koma makarantun kudi a nan gida da kasashen waje!
Wani abin takaici  shi ne wai shugaban kasar yana da digiri ta uku kuma duk a kasar nan ya yi su! Kuma tsohon malamin jami’a ne, kuma da shi kansa shugaban kasar da malaman jami’o’i duk a kasar nan suka yi karatu a matakin farko, amma dubi yadda suka bar abubuwa suka lalace! Duk da wasu mutane na da ra’ayin da malaman sun bi wata hanya ba ta yajin aiki ba, domin abin ya shafi dalibai, wadanda mafi yawancinsu ‘ya’yan talakawa ne! Bugu da kari idan kowa zai yi yajin aiki a kasar nan, kasar zata durkushe, amma da abubuwa sun gyaru! Domin ba bangaren da ake biya masa bukata yadda ya kamata! Kowane bangare na bukatar yajin aiki a kasar nan!
Ina goyon bayan malaman jam’ia su ci gaba da yajin aikin, domin haka ne zai sa a waiwaye su, a biya bukatunsu koda karin albashi ne, ta yadda wannan zai zama yajin aikin jami’o’i na karshe! Kuma wannan dama ce ta nan gaba duk wanda zai tsaya takara shugaban kasa ya fayace matsayinsa game da harkar ilimi da irin kason da zai ba ilimi a kasafi kafin dalibai da malamai su zabe shi.
Yayin da sanatoci da sarakuna suka shigo don su sansanta, maganar ita ce me zai hana kowa a cikin sanatoci su dawo da ‘ya’yansu makarantun gwamnati. Domin a gani na idan gwamnati da gaske take ta cika alkawarinta! Na biyan duk kudin da za su isa wajen daukar nauyin ilimin jami’o’i Najeriya.

Buhari Daure
+2347035986444
Muryar Talaka, Jihar Katsina
[email protected]

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50