Yadda za a shawo karshen satar shanu
Salam Edita, don Allah Ka ba ni dama a wannan jarida ta mu mai farin jini don in yi tsokaci a kan yadda barayin shanu suke yawan damun fulani makiya da satar shanu. Da za a daina sayar da shanu a ko’ina na wani dan lokaci, watakila da an shawo kan al’amarin. Gaskiya irin yadda […]
Salam Edita, don Allah Ka ba ni dama a wannan jarida ta mu mai farin jini don in yi tsokaci a kan yadda barayin shanu suke yawan damun fulani makiya da satar shanu. Da za a daina sayar da shanu a ko’ina na wani dan lokaci, watakila da an shawo kan al’amarin. Gaskiya irin yadda ake yawan kashe fulani a Jihohin Nasarawa da Zamfara da Kaduna da sauransu abin ya isa haka nan.
Sako daga 09033322295
Salam Edita, ka ba ni dama na yi sharhi a kan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasar Kamaru. Allah Ya sa wannan ziyara ta kawo mana alheri musamman a bangaren yaki da ’yan Boko Haram Da fatan kasashen Cadi da Nijar da Kamaru za su ba shi hadin kai wajen yaki da wadannan ’yan ta’adda.
Daga Kwamared Nura Bello Daraja Kaset Gusau Jihar zamfara. 08032558025.
Gaba dai,
gaba dai sojojin Najeriya!
A gaskiya mu ’yan Najeriya mun yaba maku ganin yadda kuka kwato garin Dikwa da ke Borno daga kungiyar Boko Haram. Muna rokon Allah Ya cigaba da taimakonku.
Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999
Yabon Gwani
ya zama dole!
Na fara da wannan ne, doman in yi jinjina, ga hukumomin lafiyar Najeriya, bisa kawar da cutar Polio, da aka kwashe shekara daya, ba tare da samun ko da mutum daya da ke dauke da cutar shan inna, watau Polio ba. Shakka babu wanna babbar nasara ce ga hukumar lafiya ta Najeriya. Daga karshe nake rokon Allah Ya sa karshen wannan cuta kenan a Najeriya da Afirka da ma a duniya baki daya, amin.
Daga Aminu Dankaduna Amanawa. 09035522212:
Barka da sallah
Edita ka ba ni dama in taya daukacin al’ummar Musulmi musamman ’yan uwana masu karatun jaridar Aminiya barka da bikin karamar sallah. Da fatan kowa ya yi bikin karamar sallah lafiya. Allah Ya sa mun yi azumin watan Ramadan a sa’a. Allah Ya sa mu ga zagayowar shekara mai zuwa lafiya, amin.
Daga Honorabul Shamsu Muhammad Katsina 07039878892 ko 08032627533
Nasiha Ga Sambo Dasuki
Salam, Edita ina maku fatan alheri. Don Allah ka ba ni fili don na yi tsokaci a kan Sambo Dasuki. Komai ya yi zafi maganinsa Allah. Sannan kowa ya debo da zafi, bakinsa.
Sambo a guje wa duniya a koma ga Allah. Daga Kamal Kabir Kabo
A yi hattara da ’yan damfara
Ina kira ga al’umma da su yi hattara da wadansu bata gari masu cewa mutane su rika yin sadaka da dabino za su yi kudi. Babu wanda zai iya azurta wani sai Allah. Akan haka ne suke yaudarar mutane. Allah Ya shirye su, amin.
Daga Sa’idu Ishak dan Kanan Gora, Jihar Nasarawa
Masoyin Buhari
Aminiya ni ne masoyin Buhari na daya, da ya sanni da na ji dadi amma haka Allah Ya so. Amma ina yi wa mutanen Najeriya albishir da cewa yanzu bukatarmu ta biya na samun Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Daga Habibu Tsohon Soja ’Yan Lemo Kano
Mun yi murna da sabon DPO a Tafa
Edita, ina so ka mika min sakon gaisuwata ga sabon shugaban ’yan sandan yanki (DPO) na garin Tafa. A gaskiya mun yaba da yadda wannan jami’in ’yan sanda yake gudanar da aikinsa bisa tsari da kamanta gaskiya. Fatanmu dai jama’ar gari su cigaba da ba shi hadin kai da goyon baya.
Daga Muhammad Sani wanda aka fi sani da Sani Bizy Boy Tafa 08061502594
Kira Ga Gwamnatin Zamfara
Mun kira ga gwamnan Jihar Zamfara da ya yi wa Allah ya rika biyan albashin ma’aikata a kan lokaci. Yanzu babu albashi kuma babu kudin hutu. Allah Ya ba shi ikon gyarawa.
Daga Maryam Ibrahim Gusau 09030402291
Shawara ga Buhari
Aminiya ina son ku aika da wannan sako ga shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari wannan masifa ta Boko Haram da ta dame mu a Arewa me zai sa ba za a nemo ’yan mazan jiya ba da suka je ECOMOG a hada su da matasan sojojin da suke kasar nan don su yake su>
Daga S. Ya’u DGW PH 07033145873
Yabo ga Gwamnan Jigawa
Salam, Aminiyua uwar labari, don Allah ku mika min sakon jinjina ga Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar. Don Allah ka da ka rika jin zugar munafukai ya cigaba da ayyukan alherin da ya sanya a gaba.
Daga Sani Idris Tela Dilmari KKM JG
Jaje ga Kanawa
Salam Edita don Allah ka ba ni dama in yi wa al’ummar Jihar Kano jaje dangane da ibtila’in da ya faru na ambaliyar ruwan sama, wanda hakan ya janyo asarar miliyoyin kudi sakamakon shigar ruwa shagunan wasu musamman a wasu kasuwanni kamar kantin Kwari da kasuwar Kurmi. Bayan haka ruwan ya ruguza gidaje da dama har da asarar rayuka. Hakika wannan ba karamin ibtila’i ba ne sai dai mu yi ta addu’ar Allah Ya mayar wadanda suka yi asara da alheri. Marasa lafiya kuma Allah Ya ba su lafiya. Wadanda suka rasu Allah Ya jikansu. Daga Aminu Abdu Baka Noma, Sani Mainagge, Kano 08028505350.
Ga Shugaba Buhari
Edita ka ba ni dama in bai wa ’yan Najereiya da Shugaba Buhari shawara kan gyaran kasa. Ya kamata al’umma kowa ya gyara kansa, mu daina aikata miyagun ayyuka, kowa ya zama dan kasa nagari. Mai girma Shugaban kasa kai kuma ka sanya tallafi ga rayuwar al’umma, musamman ta hanyar amfani da kudin sata da aka kwato don ya zama darasi ga sauran ’yan Najeriya. Allah Ya taimake mu. Amin. Daga Isyaku Umar, Jihar Jigawa 08061572360.