Yadda za a yi amfani da ganyen shayi wajen gyaran fata
Yadda za a yi amfani da ganyen shayi a fata
Ganyen shayi na da amfani a jikinmu domin shan sa na kara lafiya da kuma rage gautsin fata. Kowane ganyen shayi na da nasa amfani a jiki amma koren ya fi muhimmanci.
Za a iya shafa ganyen shayin a fuska. Koren ganyen shayi na kare fata daga saurin tsufa.
- Za a dage kidayar jama’a zuwa watan Mayu
- Gwamnatin Kaduna za ta rabar da shagunan Kasuwar Barci
Bayan haka, yana kuma kare jikinmu daga cututtuka da dama. Yawan shan koren ganyen shayi na sanyawa a ga mutum kamar saurayi, nan kuwa ya hada shekaru.
Hanyoyi da za a iya amfani da koren ganyen shayi:
- Amfani da koren ganyen shayi na rage warin numfashi: A tafasa ganyen shayi. Bayan haka, sai a jira na tsawon mintuna 30. Sai a rika amfani da shi wajen wanke baki. Yin hakan na hana datti zama a kan hakori. Kuma zai kare bakin daga wari.
- Shan shayin na rage kiba: Za a iya shan shayi safe da yamma domin rage maikon jiki.
- Koren shayi na rage tunbi ga macen da ta taba haihuwa da wadda ba ta taba haihuwa ba: Shan ganyen shayi mara suga akalla sau biyar a rana na matukar rage tunbi ga mata, musamman ma macen da ta taba haihuwa. Gara a gyara tun da ba a kwalliya da tunbi. Yana da kyau a jure na tsawon watanni biyar, za a yi matukar mamaki da yadda tunbi zai shanye.
- Ganyen shayi na magance ciwon ido: A sanya ganyen shayi a firij na tsawon mintuna biyar, sannan a rika dorawa a kan idon har sai ya narke. Yana rage ciwon ido mai zafin nan. Yana gyara fuska:
- A samu koren ganyen shayi sannan a zuba burbudin a cikin zuma sai a rika shafawa a fuska na tsawon mintuna 20, akalla sau biyu a rana, safe da yamma. Yin hakan na magance fesowar kurajen fuska.
- Za a iya amfani da koren ganyen shayi a fuska: Akan sanya wannan ganyen a man shafawa, domin ganyen na kunshe da sinadarin bitamin C da A da kuma E. Amfani da ganyen na rage maikon fuska kuma fuskar tay i santsi yadda ko alamar kuraje ba za a ji ba. Za a samo mayonnaise sai a debi cokali uku daga shi. Sannan dakakken koren ganyen shayi. Za a shafa a fuska, ban da gefen idanu. Sai a bar shi na tsawon mintuna 20 sai a wanke da ruwan dumi