Saudiyya ta shirya Bikin Ranar Larabci a Amurka

Kwalejin Harshen Larabci na Sarki Salman ya shirya taro raya harshen Larabci da al’adun Larabawa a Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a kasar Amurka

Saudiyya ta shirya Bikin Ranar Larabci a Amurka

Daga harabar Majalisar Dinkin Duniya Mohammed Deif. Michael M. Santiago/Getty Images/AFP (Photo by Michael M. Santiago / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / Getty Images via AFP)

Kwalejin Harshen Larabci na Sarki Salman da hadin gwiwar Ofishin Jakadancin kasar Saudiyya da ke Birnin New York a Amurka ya shirya taro a Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya domin bikin Ranar Harshen Larabci.

Karo na Hudu a jere ke nan da ake gudanar da taron da nufin raya harshen Larabci a  manyan hukumomin duniya da kuma tallata matakan da Saudiyya ke dauka domin raya harshen wajen bunkasa al’adu da kuma kimiyya.

Taken bikin na bana, wanda zai gudanar a ranar Litinin 9 ga Dismaba, 2024, shi ne ‘Harshen Larabci da Fasahar Na’ura – Bunkasa Kirkire-Kirkire tare da Raya Al’adu.

Kamfanin Dillancin Labaran Kasar Saudiya (SPA) ya bayyana cewa Ministan Raya Al’adun kasar, Yarima Badr bin Abdullah bin Farhan ne mai masukin baki a wurin taron, wanda zai karbi bakuncin manyan shugabanni da jami’an diflomasiyya.

A taron na bana za gudanar da tattaunawa kan ‘Fassarar Larabci a Majalisar Dinkin Duniya’ inda kwararru daga sassan duniya za su tattauna tare da bayar da kwas kan ‘dabarun fassarar harshen Larabci a harkoikin diflomasiyya, ga ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya.

Kazalika an shirya baje kolin kayan zayyana da al’adu da tarhin Larabawa da cigabansu, musamman daga yankin Saudiyya.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa