Yadda za a yi da Muslumin da coronavirus ta yi ajalinsa
Tun bayan da cutar coronavirus ta fara ajalin Musulmi a wasu kasashe aka fara tambaya a kan yadda ya kamata a yi da gawarsu. A bisa tanade-tanaden addinin Musulunci dai, idan Musulmi ya riga mu gidan gaskiya za a yi masa wanka, a yi masa sutura – ma’ana a sanya masa likkafani – a yi […]
Tun bayan da cutar coronavirus ta fara ajalin Musulmi a wasu kasashe aka fara tambaya a kan yadda ya kamata a yi da gawarsu.
A bisa tanade-tanaden addinin Musulunci dai, idan Musulmi ya riga mu gidan gaskiya za a yi masa wanka, a yi masa sutura – ma’ana a sanya masa likkafani – a yi masa sallah, sannan a je a binne shi.
Dukkan wadannan matakai suna bukatar taba gawar; amma kuma masana da hukumomin lafiya na gargadi kada a taba mai dauke da cutar don kada a kamu.
To yaya za a yi ke nan? Wannan ce tambayar da za mu yi yunkurin amsawa a nan a takaice.
Wankan gawa
Idan mutum ya rasu kuma gawarsa ta zamo ba za ta tabu ba, saboda wata annoba da za a iya dauka daga gare ta, ya wajaba a samar da wani shamaki da zai katange mutane daga taba gawar.
Misali shi ne a samu wasu kayan aikin asibiti kamar su safar hannu da rigunan kariya da takunkumin baki kafin a kai ga gawar.
In zai yiwu a yi mata wanka saboda wannan kariya, sai a yi wa gawar wanka kamar yadda shari’a ta nuna.
Wato a fara da yi wa gawar alwala, sannan a yi mata wanka irin na tsarki.
Idan wanka ba zai yiwu ba, saboda ana jin tsoron daukar wannan cuta daga gare ta, sai a yi taimama a guraben alwala kawai, hakan ya wadatar.
Ko kuma idan ta rube ko ta kone ta yadda babu gabban da za a yi taimamar sai a yayyafa wa gawar ruwa a matsayin wanka tare da niyya.
Kusantar gawar
Wajibi ne a kiyaye tare da bin duk wata hanya da za ta kare sauran mutane daga kusantar gawar da za a iya daukar cuta daga gare ta, yayin yi mata wanka ko taimama ko sallah ko binne ta.
Bayan takaita yawan mutanen da za su yi mata sallah, a tabbatar an ajiye gawar a inda ba za a iya daukar cutar daga gare ta ba, kamar cikin mota ko akwatu ko wani karfe ko gilashi.
Sannan yayin sallar mutane su guji gwamutsuwa, ma’ana su yi nesa da juna gwargwadon yadda masana kiwon lafiya suke bayar da shawara a yanzu.
Sallar jana’iza
Sallar Jana’iza farali ce ta kifaya wato wadansu suna dauke wa wadansu.
Don hakal kada mutane su kallafa wa kansu cewa lallai sai sun halarci jana’izar wane saboda dan uwansu ne ko aboki ko amini.
Idan ma akwai jami’an kiwon lafiya Musulmi da za su iya gudanar da wannan sallah ba lallai ne na kusa da mamacin su ce sai sun sallaci gawar ba.
Wadanda suke jin lallai suna bukatar yi wa mamacin sallah amma lalura ba ta bari sun halarci yi masa sallah ba, suna iya yin salatul gha’ib, wato sallar jana’iza ga gawar da ke nesa ko aka riga aka binne ta, ba tare da sun yi cinkoso ba.
Ko rukunin mutum kadan su je inda aka binne mamacin su yi masa sallar suna masu kiyaye hada kafada da juna tare da bayar da tazarar da likitoci suka yi umarni.
Ko kuma su yi masa addu’a a daidaikunsu a duk inda suke. Ba aikin lada ba ne ko burgewa mutum ya jefa rayuwarsa a hadarin kamuwa da cutar da ake dauka daga mutane don kawai ya aikata wani aiki da bai zama farilla a kansa ba, kamar sallar janaza.
Binne gawar
Sannan a kyale ma’aikatan lafiya da suke da kayan kariya su dauki gawar su kadai zuwa inda za a binne ta, kamar yadda za a kyale su su dauke ta su sanya ta a kabari.
In da bukatar a nusar da su bai wuce a je da mai nusarwar ko mutane kalilan da ba za su jawo cunkoso a irin halin da ake ciki ba.
In kuma mutane da yawa suka raka gawar to su warwatsu nesa-nesa da juna domin Amru bin Ausu (RA) ya ce annoba kamar wuta ce, kuma mutane su ne makamashinta, don haka in suka yi nesa da juna sai ta rasa wannan makamashi.
Don haka bai dace mutane su cunkusu a bakin kabari a irin wannan hali ba.
Ya wajaba mutane su tuna ba gawar kadai ce abar gudu game da wannan cuta ba, a’a cikin mutanen da suka taru a iya samun wanda ke dauke da cutar amma ba ta bayyana ba sai ya zamo ya harbi wadansu.
Sannan mutane su yi nesa da jami’an kiwon lafiyar da suka taba gawar kada su gwamutse su balle su kai ga taba kayan da suke sanye da su.
Su ma jami’an kiwon lafiyar su yi nesa-nesa da mutane tare da hana mutanen kusantarsu da nuna musu illar yin haka.