Yadda za a yi jana’izar mutane 37 da sojoji suka gano gawarsu a Yobe

Waɗanda gawarwakinsu suka ruɓe za a binne su ne a garin Mafa inda Boko Haram ta yi musu kisan gilla

Yadda za a yi jana’izar mutane 37 da sojoji suka gano gawarsu a Yobe

Jana’izar Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri

A safiyar Talata za a yi jana’izar mutane 37 da kungiyar Boko Haram ta yi wa kisan gilla da sojoji suka gano gawarwakinsu a garin Mafa na Jihar Yobe.

Da misalin ƙarfe 10 na safe za a sallaci mutanen su 37 a Fadar Sarkin garin Babangida, fadar Ƙaramar Hukumar Tarmuwa.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa Aminiya cewa ragowar waɗanda gawarwakinsu suka ruɓe, za a binne su ne a garin Mafa.

Sojoji sun gano gawarwakin mutanen ne bayan harin ƙungiyar a garin Mafa fa ke Karamar Hukumar Tarmuwa.

A ranar Litinin da dare aka kai su aka ajiye a Babban Asibitin Babbangida bayan an gano su.

Mataimakin Gwamnan Yobe, Barde Idi Gubana, zai jagoranci manyan jami’an gwamnati wajen halartar jana’izar.

Daga nan kuma za a wuce maƙabarta a sanya su a makwancinsu.

A yammacin ranar Lahadi ne mayaƙa kimanin 250 ɗauke da muggan makamai a bisa babura suka far wa garin Mafa da hari.

Mazauna garin da suka tsallake rijiya da baya sun ce mutanen da aka kashe a harin sun kai 87, kuma yawancinsu mata da kananan yara da tsofaffi ne.

Shaidun sun bayyana cewa mayaƙan sun kuma sace matasan garin da dama, suka gidaje da shaguna kimanin 1,000.

Sun kuma yi awon gaba da kayan abinci da dukuyiy daga harin wanda yanzu ya zama kufai.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana