Yadda za a yi kwalli ya lokacin damina

Mata da dama ba su cika son yin kwalliya a lokacin damina ba. Domin suna tsoro ka da a fara ruwan saman da zai wanke musu wannan kwalliyar, ko kuma ta cabe musu ita. Sau da yawa ana tambaya wai shin wace irin kwalliya ce ta dace a yi a lokacin damina? Don haka ne […]

Yadda za a yi kwalli ya lokacin damina

Mata da dama ba su cika son yin kwalliya a lokacin damina ba. Domin suna tsoro ka da a fara ruwan saman da zai wanke musu wannan kwalliyar, ko kuma ta cabe musu ita. Sau da yawa ana tambaya wai shin wace irin kwalliya ce ta dace a yi a lokacin damina? Don haka ne a yau na kawo muku yadda za a magance wadannan matsalolin ta hanyan sauki.
•Akwai wasu irin hodar fandesho masu santsi kamar mai. Irin su ne ya kamata a yi amfani da su a lokacin damina, domin  ko da ruwan ya taba fuskar, ba za ta wanke fuskar ba. A nemi irin wannan hodar fandesho din domin samun sauki ga lamarin
•Akwai wata ‘waterproof mascara’ abin nufi a nan shi ne ruwa ba ya ratsa cikinta. Irin shi ne ya kamata ‘yan mata da manyan mata na amfani da su a wannan lokacin. Idan ba a yi la’akari da samin irin wannan mascara ba to a sani cewa kwalliyar za ta cabe sosai.
•Kada a manta da lema a duk lokacin da za a fita domin ba za a san lokacin da ruwan zai sauko ba.
•A kasance tare da abin rufe kai. Domin yawan sanya ruwa a gashi ba karamin karya gashin yake ba. Don haka sai a samo wani abu da zai rufe kan yadda ruwan ba zai ratsa shi ba.
•Yana da kyau kuma a san irin takalmin da za a sa saboda jikewa daga ruwan sama. Ana son amfani da takalmin roba, wanda ba zai sa a fadi ba, saboda santsin wuri a lokacin ruwan sama.
•A samu kaya na mutunci wadanda za a sanya a wannan lokacin saboda wani lokacin idan aka jike, kuma idan har tufafin wasu matsatsu kaya ne, sai a ga surar mutum kaf ta bayyana a fili. Yana da kyau mace ta san yadda za ta kula da kanta.