Gaza: Yadda za a yi musayar fursunonin Palasdinawa da Isra’ila

Falasɗinawa 1,650 ake sa ran za su fito daga gidajen yarin Isra’ila bayan yarjejeniyar zaman lafiyar Hamas da gwamnatin Isra’ila ta fara aiki

Gaza: Yadda za a yi musayar fursunonin Palasdinawa da Isra’ila

Aƙalla Palasdinawa 1,650 ake sa ran za su shaƙi iskar ’yanci daga gidajen yarin Isra’ila a yayin da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Hamas da Isra’ila za ta fara aiki karfe 6.30 na safiyar ranar Lahadi.

Isra’ila za ta sako Palasdinawa da take tsare da su ba tare da wani laifi ba ne, a yayin da Hamas za ta sako mutane 33 daga cikin waɗanda ta kama a Isra’ila a harin ranar 7 ga Oktoba, 2023 — a matsayin kashin farko na yarjejeniyar.

Aƙalla mutum 100 ne Hamas ta kamo daga Isra’ila, kuma ɓangarorin sun amince za a yi musayar a bisa adadin da suka yarda a tsakaninsu a yayin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka ƙulla a ranar Laraba.

Daga ciki, Isra’ila za ta sako Palasdinawa 110 da ta yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da-rai, a yayin da Hamas za ta sako mata mutum tara da suka jikkata daga cikin mutanen da ta kamo a Isra’ila.

Sannan Hamas za ta yi musayar ’yan Isra’ila maza ’yan shekaru sama da 50 guda tara, inda Isra’ila za ta ba ta Palasdinawa 27 a madadin kowane mutum daya; ko mutum uku da ke zaman rai-da-rai a kan kowane Ba’israle guda.

Tuni hukumomin Isra’ila suka fitar da jerin sunayen mata da ƙananan yara 95 daga cikin Palasdinawan da za su saki.

Jerin sunayen ya nuna akasarin waɗanda za a saki sojojin Isra’ila sun kama su ne bayan mayar Isra’ila a Gaza bayan harin 7 ga Oktoba. Hasali ma ƙasa da mutum 10 a cikinsu ne aka kama kafin nan.

Palasdinawa sama da 10,000 ne ke tsare a gidajen yarin Isra’ila tun kafin lokacin.

Za a yi musayar ne na bayan a ranar Juma’a da dare, Majalisar Dokokin Isara’ila ta amince da sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da Gwamnatin Fira Minista Benjamin Netanyahu ta ƙulla da ƙungiyar Hamas ta Palasdinawa.

Amincewar ya buɗe ƙofar fara aiki da yarjejeniyar zaman lafiyar daga ranar Lahadi, inda za a fara musayar fursunonin yaƙi a tsakanin ɓangarorin biyu.

Majalisar ta samun amince da yarjejeniyar ce bayan shafe watanni ana tattaunawa har cikin dare, duk da cewa wasu ministoci biyu sun kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa.

Tun da farko, Ofishin Fira Minista Benjamin Netanyahu ya sanar cewa Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da yarjejeniyar da aka fara ƙullawan da cewa, “ta dace da manufar yaƙin.”

Amincewar Majalisar na zuwa ne awanni bayan ƙungiyar da ofishin Netanyahu, kowannensu ya sanar cewa ya kammama sauran abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa — kwana biyu bayan ƙasashen Masar da Qatar da Amurka da suka shiga tsakani sun sanar da ƙulla yarjejeniyar a ranar Laraba.

Fira Ministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdul Rahman Al Thani ya ce yarjejeniyar za ta fara ranar Lahadi idan majalisar dokokin Isra’ila ta amince.

A wancan lokacin Netanyahu ya bayyana cewa ƙasarsu na ƙoƙarin kammala aiki kan bayanan yarjejeniyar.

Daga bisani ya jinkirta zaman ranar Alhamis domin amincewa da yarjejeniyar, saboda zargin Hamas da neman amfani da damar.

Hamas dai ta ce a shirye take ta bi ka’idojin yarjejeniyar.

Duk da cewa gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar, dole sai ta samu amincewar Majalisar Tsaro da majalisar ministoci.

Sai dai ministoci biyu masu ra’ayin riƙau, waɗanda kuma mambobin majalisar tsaron ƙasar, Itamar Ben Gvir da Bezalel Smotrich, sun ƙi amincewa da yarjejeniyar tare da barazanar yin murabus.

Sai dai duk da haka sun ce ba za su haɗe da ’yan adawa ba wajen yaƙar gwamnati, muddin aka ci gaba da yaƙin bayan makonni shida, lokacin da za a kammala musayar fursunonin a wa’adin rukunin farko na yarjejeniyar.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya bayyana cewa ranar Lahadi za a fara musayar fursunonin yaƙi, inda Hamas za ta sako mutum uku.

Dubban Falasɗinawa da ’yan Isra’ila dai sun bayyana farin cikinsu bayan an sanar da ƙulla yarjejeniyar ta ranar Laraba 15 ga Janairu, 2025.

HOTUNA: Tankar mai ta yi bindiga a Dikko Junction

An kashe manyan alƙalai 2 a harabar Kotun Ƙolin Iran

’Yan Yahoo sun harbe jami’in EFCC har lahira a bakin aikinsa

Farashin kayan abinci ya faɗi warwas a Neja