Yadda za ki goge kwalliyarki kafin ki kwanta

Sau da yawa mata ba su cika wanke fuskarsu kafin su kwanta ba, kuma ba su fahimci illar hakan ba. Yana da kyau mata su rika wanke fuskarsu kafin su kwanta. Domin idan suka kwanta da kwalliya fuskarsu, hakan na kawo kurajen fuska. Akwai hanyoyi da dama wadanda ya kamata mata su bi don goge […]

Yadda za ki goge kwalliyarki kafin ki kwanta

Man zaitun a kwalbaSau da yawa mata ba su cika wanke fuskarsu kafin su kwanta ba, kuma ba su fahimci illar hakan ba. Yana da kyau mata su rika wanke fuskarsu kafin su kwanta. Domin idan suka kwanta da kwalliya fuskarsu, hakan na kawo kurajen fuska. Akwai hanyoyi da dama wadanda ya kamata mata su bi don goge datti da maiko da kuma kwalliyar fuskarsu kafin su kwanta barci.
·         A samu man zaitun mai kyau ba wanda aka surka shi da wani abu ba. A samu ruwa da murta ko kwalba wanda za a zuba hadin a ciki. Sannan sai a zuba zaitun cikin cokali daya ko kuma (daidai yadda ake so) da ruwan a cikin kwalba. Za a iya cika kwalbar da man zaitun da kuma ruwa.
·         Sai a rufe kwalbar da murfinta, sannan a girgiza don ruwa da man zaitun su gaurayu sosai.
·         Yana da kyau a gwada hadin a fatar hannu. Domin wadda fatarta ba ta dace da wannan hadin ba, za ta ga kuraje sun feso mata. Sai a zana gazal a fatar hannu a hada hadin sai a goge da shi. Idan bayan minti 30 ba a ji canjin yanayi ko wata illa ba, to za a iya amfani da shi a fuska. Bayan an gama, sai a rufe kwalbar.
·         A duk lokacin da za a yi amfani da hadin, ya kamata a girgiza kwalbar domin hadin ya gaurayu sosai.