Yadda za ki gyara furfurarki
Fitowar furfura ko farin gashi akan mace yana zama wani abu na jin kunya ko rashin so ga wasu mata. Mata da yawa suna fargabar ace an wayi gari furfrura ta fito musu. Yayin da aka ce furfura ta fito wa wasu matan, sai ka ga sun daina gyaran gashinsu, wai a cewarsu tunda gashin […]
Fitowar furfura ko farin gashi akan mace yana zama wani abu na jin kunya ko rashin so ga wasu mata. Mata da yawa suna fargabar ace an wayi gari furfrura ta fito musu. Yayin da aka ce furfura ta fito wa wasu matan, sai ka ga sun daina gyaran gashinsu, wai a cewarsu tunda
gashin ya yi fari, to babu amfanin yi masa gyara na musamman.
Yin maganin furfura tamkar magance damuwar sauran sassa na jiki ne ko kuma mu ce ya danganta da yadda ake kula da gashin ne. Wani abu da mata ba su sani ba shine ita furfura ba abu ne dake fito miki da tsufa ba ya danganta da yadda kike kula da gashinki.
Akwai hanyoyin da za a bi wajen gyara furfura:-
A Wanke gashi da man wankin gashi mai kyau, wanda kuma yake da maiqo.
Ki riqa shafa man wankin gashi a jikin fata, sai ki bar shi tsawon mintuna sannan sai ki wanke. Daga nan sai ki xauko kwandishina ki sa a gashin. Ki bar shi tsawon minti xaya zuwa biyu sannan sai ki sa ruwa ki xauraye.
. A kare gashi daga rana. Waannan ba wai lokacin rani kaxai ba har ma da lokacin sanyi. Ida ana barin gashin a buxe zai bushe ya zama babu kyawun gani. Don haka a duk lokacin da za ki fita ki rufe kanki.
. Za ki zavi man rinin gashi mai kyau wanda ya dace da gashin . Idan kika sa rinin zai taqaita yawan wanke gashinki, domin kada gashin ya koxe.
Idan ma za a wanke gashin ya kamata a wanke shi da ruwan zafi ko ruwan xumi.
. A riqa shafawa gashin mai, mai kyau don yayi laushi da sheqi misali
man kwakwa da sauransu.