Yadda za ki inganta kwalliyarki da ‘ya’yan itatuwa
Ko kun san cewa duk ababen da suka kunshi ’ya’yan itatuwa na da muhimmanci a wajen gyaran jiki. Akwai ’ya’yan itatuwa ko kwallonsu da ke inganta kwalliyar mace ko namiji. Don haka a yau na kawo muku. Domin idan akwai wadanda suke son magance wata matsalar fata, ko na sanya murya zaki su san yadda […]
Ko kun san cewa duk ababen da suka kunshi ’ya’yan itatuwa na da muhimmanci a wajen gyaran jiki. Akwai ’ya’yan itatuwa ko kwallonsu da ke inganta kwalliyar mace ko namiji. Don haka a yau na kawo muku. Domin idan akwai wadanda suke son magance wata matsalar fata, ko na sanya murya zaki su san yadda za su magance matsalolinsu.
Domin zakin murya
Za a samu ganyen mangoro sannan a tafasa a ruwa ana sha kullum domin samun zakin murya. Akwai mata masu babbar murya da in suka yi magana sai a zata namiji ne, wannan na iya magance musu tasu matsalar. Za a iya shan wannan ruwa sau biyu ko uku a rana.
Domin dafewar fata
A samu kwallon dabino kamar kwallo 10 sai a gasa san nan a daka su yi laushi. Bayan haka, sai a samu man kwakwa a hada garin kwallon dabinon da shi. Sai a rika shafa wannan maganina inda aka kone.
Domin kawar da furfura
A samu ganyen kori da ganyen aloe bera da ganyen lalle. Sai a dakasu tare a wuri daya. Bayan an yi haka, sai a shafa a gashi mai furfura. Sannan a jira na rabin awa kafin a wanke. Yana da kyau a rika amfani da wannan hadin kamar sau 3-4 a mako.
Domin samun fata mai laushi
A samu nutmeg da madara bayan an nika nutmeg, sai a zuba madara a ciki. Sai a shafa a jiki kullum kafin a yi wanka. A bari ya bushe a fatar jiki kafin a wanke. Yin haka kullum na sanya fata sulbi.