Yadda za ki magance gashin da ba ya kan ka’ida

Wadansu mata suna fuskantar damuwa sakamkaon wani gashi da ke tsiro musu a wasu wurare da ba a saba da ganin gashi a wurin mata ba. Misali gemu da kuma saje. Bincike ya nuna cewa akan samu mata biyar daga cikin 100 da ke da matsalar wannan fitowar gashi. Irin wannan gashi da ke tsiro […]

Yadda za ki magance gashin da ba ya kan ka’ida

Wadansu mata suna fuskantar damuwa sakamkaon wani gashi da ke tsiro musu a wasu wurare da ba a saba da ganin gashi a wurin mata ba.

Misali gemu da kuma saje. Bincike ya nuna cewa akan samu mata biyar daga cikin 100 da ke da matsalar wannan fitowar gashi. Irin wannan gashi da ke tsiro wa mata yakan sa matan cikin damuwa wajen ganin sun samu mafita.

Hakan ya sa muka kawo wasu hanyoyi da macen da ke da irin wannan matsala za ta bi ta samu mafita daga matsalar.

Aski: Daukar hanyar aske gashin da ke fitowa ita ce ta fi sauri da sauki wajen tafiyar da gashin. Shi wannan askin ana yin sa ne kamar yadda aka saba aske kowane gashi. Sai dai wannan askin ya fi tafiyar da gashin gaba daya.

Yin amfani da mai: Akwai mai ire-iri da aka yi su wdaanda aka fi sani da man aski. Irin wadannan nau’o’in mai ana shafa su  a wajen da gashin ya fito a bar shi na tsawon ’yan mintoci. Daga nan sai a wanke za a ga gashin duk ya fice.