Yadda za ki magance kaikayin fata
Sau da dama akan ga mutun na yawan soshe-soshe. Hakan na faruwa ne sakamakon cizon sauro ko kudin cizo ko kuma cizon wadansu kwari. Yawan soshe-soshe na lalata fata, inda a wani lokaci kuraje kan feso, ko kuma fata ta yakushe. Fata kuwa tana bukatar kulawa ta musamman, domin idan babu fata mai kyau, kyawu […]

Sau da dama akan ga mutun na yawan soshe-soshe. Hakan na faruwa ne sakamakon cizon sauro ko kudin cizo ko kuma cizon wadansu kwari. Yawan soshe-soshe na lalata fata, inda a wani lokaci kuraje kan feso, ko kuma fata ta yakushe. Fata kuwa tana bukatar kulawa ta musamman, domin idan babu fata mai kyau, kyawu zai buya. A wannan makon mun kawo miki hanyoyi daban-daban wadanda za ki bi don magance kaikayin fata.
· Ki hada man zaitun da zuma, sannan ki shafa a wurin da yake miki kaikayi na tsawon minti 30, daga nan ki wanke.
· Ki samo kwai 3, bayan kin fasa su sai ki cire gwaiduwar, daga nan ki kwaba farin ruwan kwayayen da tankadadden garin masara. Bayan nan sai ki shafa a wurin da yake miki kaikayi, sannan ki bar shi na tsawon minti 30 kafin ki a wanke da ruwan dumi.
· Ki markada mangwaro da gwanda ba tare da kin cire fata da kuma kwallonsu ba. Bayan haka, sai ki tace ruwan, daga nan ki shafa a wurin da yake miki kaikayi. Bayan kin shafa sai ki bar shi zuwa minti 10, daga nan ki wanke da ruwan dumi.
· Za ki iya samo garin nutmeg sai ki hada shi da tafasashen nono, sannan ki shafa a wurin da yake miki kaikayi. Bayan awa 1 sai ki wanke.
· Lemon tsami ma na magance kaikayin fatar jiki musamman ma na cizon sauro. Abin da ake bukata shi ne, ki shafa ruwan lemon tsami a wurin da yake miki kaikayi. Bayan kamar miniti 15 sai ki wanke da ruwa mai dumi.