Yadda za ki magance kunan rana a fuskarki
Yawan fita rana na sanya fuska baki, ko ya canza launin fuska. Sai ki ga fuska ta yi baki, ta wani gefen kuma sai ki ga ta yi haske, wato dai fuskar ta yi dabbare-dabbare. Irin wannan na bata wa mace kwalliyarta, don sai a ga kamar bilicin take yi bayan kuma ba haka ba […]
Yawan fita rana na sanya fuska baki, ko ya canza launin fuska. Sai ki ga fuska ta yi baki, ta wani gefen kuma sai ki ga ta yi haske, wato dai fuskar ta yi dabbare-dabbare. Irin wannan na bata wa mace kwalliyarta, don sai a ga kamar bilicin take yi bayan kuma ba haka ba ne. Akwai hanyoyi da dama wadanda za ki bi don magance irin wannan canji a fuskarki. Ina so ki san cewa, samun sauki sai a hankali, don haka za ki iya jarraba hakan har tsawon wata uku. Idan ba ki ga canji ba sai ki nemi wata hanya daban.
· Ki tabbata duk mayukan da za ki yi amfani da su na dauke da sinadarin ‘sun screen’ a ciki don kare kunar rana.
· Za ki iya samun ganyen Aloe bera sai ki shafa ruwan a fuskarki a kan inda ta yi dabbare-dabbare.
· Madara na kara wa wa mace kyau. Ki samu madara sai ki hada ta da ruwan sanyi, sannan ki kada sosai, bayan nan sai ki shafa a kan dabbare-dabbaren fuskarki na tsawon minti 20. Za ki iya hakan sau biyu a rana bayan awa 2 ko 4.
· Zuma na taimakawa kwarai wajen magance dabbare-dabbaren fuska.
· Man kifi (cod liber oil) na taimakawa wajen magance kunar fuska da a aka samu ta hanyar kunar rana.