Yadda za ki magance kyasbi
kyasbi mummunar cuta ne da ke addabar fata. Babban abin damuwar shi ne bai cika warkewa da wuri ba. Abubuwa da dama na sanya mutum ya kamu da kyasbi. Kamar kyankyani ko damina. Idan mutum na da fata mai gautsi, hakan na kawo kyasbi. Yadda mutum zai gane cewa ya kamu da kyasbi kuwa shi […]
kyasbi mummunar cuta ne da ke addabar fata. Babban abin damuwar shi ne bai cika warkewa da wuri ba. Abubuwa da dama na sanya mutum ya kamu da kyasbi. Kamar kyankyani ko damina. Idan mutum na da fata mai gautsi, hakan na kawo kyasbi. Yadda mutum zai gane cewa ya kamu da kyasbi kuwa shi ne, zai rika yawan jin kaikayi a fatarsa. Kuma idan ya sosa wurin sai ya ga kuraje sun feso masa. Za a iya samun kyasbi a iyalin da suke da tarihin ciwon asma (Asthma). Har yanzu ba a samu maganin da ke warkar da kyasbi ba amma akwai hanyoyi da dama wanda za a iya amfani da su don samun sauki.
Hanyoyin magance kyasbi
Mayuka da dama na magance kyasbi, misali man kwakwa da zaitun da kuma na aloe bera. Man kwakwa na dauke da sinadarin ‘fatty’ da ‘luric acid’ wadanda suke taimaka wa fata wajen magance duk cututtukan fata.
Man kwakwa da na zaitun na da amfani sosai ga fatarmu, musamman ma wajen magance kyasbi. Idan mutum yana da kyasbi, ya kamata ya daina barin jikinsa a bushe. Za a iya shafa man zaitun ko man kwakwa a wurin da kyasbin ya feso. Ko kuma a samu ruwan aloe bera ana shafawa a kan kyasbin.
Za a iya hada sakar zuma da man zaitun da man kwakwa da kuma na aloe bera a wuri daya. Sai a kwaba hadin har sai ya gaurayu da kyau kafin a shafa a kan kyasbi. Idan an shafa, sai a jira na tsawon awa daya kafin a wanke.
Muna son masu karatu su yi hakuri da irin wannan maganin, saboda duk abin da ya shafi fata, yakan dauki lokaci kafin ya warke.