Yadda za ki magance numfashi mai wari

Numfashi mai wari na samuwa ne idan mutum ya ci abinci mai wani irin dandano kamar albasa da tafarnuwa, ko kuma rashin lafiya da kuma cututtukan da suka shafi baki da hanci da makogwaro da hanji da sauransu. Wasu kan yi amfani da man goge baki da buroshi amma duk da haka idan sun yi […]

Yadda za ki magance numfashi mai wari

TuffaNumfashi mai wari na samuwa ne idan mutum ya ci abinci mai wani irin dandano kamar albasa da tafarnuwa, ko kuma rashin lafiya da kuma cututtukan da suka shafi baki da hanci da makogwaro da hanji da sauransu. Wasu kan yi amfani da man goge baki da buroshi amma duk da haka idan sun yi numfashi ko sun yi magana sai an ji wari.
Hakan ne ya sa na yi miki guzurin yadda ruwan tuffa da sinadarin apple cider binegar’ suke magance numfashi mai wari.
•    Da farko ki samu tuffa sai ki nika ta, sai ki zuba ruwan a cokali, sannan ki sha, wannan zai taimaka miki wurin narkar da abinci, ya kuma magance miki numfashi mai wari. Za ki rika yin hakan duk lokacin da kika ci abinci.
•    Bayan kin goge baki sai ki samu sinadarin ‘apple cider binegar’, sai ki gauraya shi da ruwa kadan, sai ki kurba sannan ki kuskure bakinki kamar na sakan 10. Za ki iya hakan duk bayan lokacin da kika ci abinci.
Wadannan hanyoyi za su magance miki numfashi mai wari.Sinadarin ‘Apple cider vinegar’