Yadda za ki rabu da amosanin ka
Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata. Wasu kuma sukan je shagunan wanke kai domin a magance musu wannan matsalar. Albishirinku ’yan uwana! Yau na kawo muku hanyar sauki da za ku bi don rabuwa da wannan […]
Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata. Wasu kuma sukan je shagunan wanke kai domin a magance musu wannan matsalar. Albishirinku ’yan uwana! Yau na kawo muku hanyar sauki da za ku bi don rabuwa da wannan matsalar amosanin kai. A ciki akwai ganyen kashu da lemun tsami da ruwan kwakwa da kuma kwallon mangoro.
Shin ko kun san cewa ganyen kashu na maganin amosanin ka? To, ga yadda za a sarrafa shi:
· A wanke ganyen kashu, sannan sai a daka shi a kwaba da ruwa.
· Bayan hakan, sai a shafa a fatar kai a bari na tsawon rabin awa kafin a wanke. Za a iya yin haka har na tsawon sati biyu, inshaAllah, za a sami saukin amosanin ka.
Ko kun san cewa lemun tsami ma yana warkar da amosanin ka, musamman idan an hada shi da ruwan kwakwa?
· A sami lemun tsami sannan sai a matse ruwan, sannan sai a hada shi da ruwan kwakwa.
· Sannan a shafa a fatar ka a jira na tsawon rabin awa kafin a wanke.
kwallon mangoro ma yana mangance amosanin ka. Kuma ana iya hada shi ne da madara ‘butter milk’ kamar haka:
· A bushar da kwallon mangoro, sannan a daka.
· Za a iya kwaba wannan garin kwallon mangoro da ruwa sannan a shafa a kai ko kuma da madara ‘butter milk’ sannan a shafa a fatar kai. Bayan minti 30 sai a wanke. Ana yi akai-akai, domin harkar fata sai a hankali ake samin sauki.