Yadda za ki samu fata mai laushi

Yadda za a sanya fata ta yi laushi ya danganta daga fata zuwa fata ne, akwai bushasshiyar fata, akwai mai kaushi da gautsi da kuma santsi, sannan akwai fata mai fitar da maiko. Don haka ne a wannan makon zan kawo miki hanyar da za ki bi wajen samun fata mai laushi ko da fatarki […]

Yadda za ki samu fata mai laushi

Yadda za a sanya fata ta yi laushi ya danganta daga fata zuwa fata ne, akwai bushasshiyar fata, akwai mai kaushi da gautsi da kuma santsi, sannan akwai fata mai fitar da maiko. Don haka ne a wannan makon zan kawo miki hanyar da za ki bi wajen samun fata mai laushi ko da fatarki wacce iri ce.
Kayan Hadi:
Kabewa
Yogot
Sinadarin ‘Mild Freshener-toner’
kwai
Zuma
Auduga
Yadda za a hada:
 – Idan fatarki ba bushasshiya ko marar kaushi ko marar maiko ba ce, za ki sanya ta yi laushi kamar haka: Ki samu kabewa sannan ki daka ta, za ki daka har da ‘ya’yanta; daga nan sai ki dama ta da yogot. Bayan nan sai shafa a jikinki ko fuskarki har zuwa tsawon minti 10 ko 15. Idan ba a samu kabewa ba za a iya daka gurji a hada yogot kafin a shafa a fuska ko jiki.
– Idan kuma bushasshiyar fata ce da ke, bayan kin shafa hadin kabewa da yogot na tsawon minti 10 ko 15 sai ki wanke da ruwan dumi, sannan ki sahafa wani sinadari da ake kira ‘mild freshener-toner’ a jikinki na minti 30 ko awa guda.
– Idan kuma fatarki mai fitar da maiko ce, sai ki kada kwai, sannan ki samu cokali daya zuwa biyu na zuma, sai ki zuba ruwan lemo tsami kadan, daga nan sai gauraya su, daga nan ki shafa a fuskarki. Amma idan duka jikinki za ki shafa, sai ki nemi kwai da zuma da ruwan jus din da yawa, don ya game miki jikinki. Lokacin da za ki shafa a fuskarki, sai ki kiyaye kada ya shiga idanunki. Hanya mafi sauki ita ce, ki yi amfani da auduga wajen shafawa a fuska.Kabewa