Yadda za ki yi kwalliya cikin minti 5
Idan ana batun kwalliya, to kayan kwalliya masu tsada sun fi dacewa da kowace fuska. Yana da kyau ki zabi jan-bakin da ya dace da lebbanki. Ba a cika son ki rika maka kowane irin launin jan-baki ba. Launin hodar da ta dace da fata da kuma irin kwallin da za ki gyara gira da […]
Idan ana batun kwalliya, to kayan kwalliya masu tsada sun fi dacewa da kowace fuska. Yana da kyau ki zabi jan-bakin da ya dace da lebbanki. Ba a cika son ki rika maka kowane irin launin jan-baki ba. Launin hodar da ta dace da fata da kuma irin kwallin da za ki gyara gira da su da sauransu.
A yau mun kawo miki yadda za ki yi kwalliya cikin minti 5, ba tare da bata lokaci ba.
· Jan launi ya fi dacewa da kowane irin lebe, don haka idan za ki zabi launin jan-baki, ki zabi mai jan launi, sannan ki san cewa, jan launi ma daban-daban ne. Idan ke baka ce, sai ki zabi ja, amma ba mai haske sosai ba. Domin fito da kwalliyarki.
· Kada ki manta irin ‘eye shadow’ da za ki shafa a kan fatar ido. Ya kamata launin ya kasance ya dace da launin tufafin da za ki sanya, bayan an gama kwalliya.
· Idan za ki shafa hoda, ya kamata ki san wace irin fata kike da ita. Idan ke mai gautsin fata ce, sai ki samu hoda mai maiko (fandesho), wadda ta dace da fatarki. Idan kuma fatarki ba mai gautsi ba ce, sai ki shafa hodar da ta dace da fatarki.
· Adon gira: Launin ruwan kasa ya fi dacewa da kowace irin fata. Amma idan ke baka ce sosai, za ki iya amfani da gazar baki, domin fitar da kyawun girarki. Idan ko ke ruwan tarwada ce ko fara, za ki iya amfani da launin ruwan kasa.