Yadda za ki yi kwalliya idan ba ki da lafiya

Barkanmu da sake saduwa daku a wannan filin namu na kwalliya. A yau na kawo muku yadda za kiyi kwalliya idan ba ki da lafiya . Idan nace rashin lafiya ina nufin wadda batayi tsanani ba. Bai  kamata a rika barin fuska da jiki da datti ba don kawai ba’a da lafiya. Idan aka tsaftace […]

Yadda za ki yi kwalliya idan ba ki da lafiya

Barkanmu da sake saduwa daku a wannan filin namu na kwalliya. A yau na kawo muku yadda za kiyi kwalliya idan ba ki da lafiya . Idan nace rashin lafiya ina nufin wadda batayi tsanani ba. Bai  kamata a rika barin fuska da jiki da datti ba don kawai ba’a da lafiya. Idan aka tsaftace jiki ana jin sauki kuma hakan zai iya taimakawa wajen sanya sauki a ciwo. Dole ne a kasance masu tsafta a kodayaushe domin taimakawa lafiyar jiki. 

Fandesho; idan rashin lafiyar ta sanya kumburin fuska dasu idanu, yana da kyau a kasance tare da fandesho wadda zai dan boye kumburin fuskar. Bayan anyi wanka sai a samo fandesho a shafa a wajajen da suka kumbura . Yin hakan na dan dadawa fuskar haske.

kankara; idan an kasance ana fama da ciwon ido, yana da kyau a samu kankara a sanya a leda sannan a lullube ta da tawul sannan a dora tawul din akan idanuwan da suka kumbura na tsawon mintuna goma. Hakan zai taimakawa idanu wajen sabe kumburin.

Ruwa; ruwa na da mahimmanci a rayuwar dan Adam. Rashin shan isasshen ruwa na sanya gautsin fata karyewar gashin kai da dai makamancinsu. Yana da kyau a kasance ana shan shayi ko ruwa a lokacin da ba a da lafiya da kuma shafa man jiki domin rage gautsin fata.

Man baki; amfani da man baki yana karawa majinyata kyau. Yana da kyau a rika shafa man basilin a labba domin hana bushewa. Ko kuma a samu wata kala da zata karawa labban kyau  sai a yawaita shafawa domin sanya kyawun fuska.

Kwalli; kwalli na dadawa idanu haske. Yana da kyau a rika shafasu a wannan lokutan domin sanya idanu haske da kuma bayyanar dasu.

Fandesho da nayi bayani a kai ina nufin ba sai an maka ta sosai ba. Za’a iya shafata sama-sama ma ya isa. Dama domin a boye wajajen da ya kumbura a fuskar ne.

Idan mutum yaga cewa ba zai iya yin wadannan abubuwan da na lissafo ba, yana da kyau ya zauna a cikin gida yayi jinyar har sai ya warke bakidaya kafin ya fito waje. Dama muna magana ne akan rashin lafiya mara tsanani.