Yadda za ki yi kyau ba tare da yin kwalliya ba
Mace a koda yaushe damuwarta shi ne yadda za ta ganta ta iya kwalliya da ado. Kuma tana son a duk inda ta shiga idanu su bita da kallo domin ta samu tabbacin cewa ta yi kyau ta kuma iya daukar hankali. Ko kun san cewa yawan shafe-shafe na bata kyaun fatar ‘ya mace? Domin […]
Mace a koda yaushe damuwarta shi ne yadda za ta ganta ta iya kwalliya da ado. Kuma tana son a duk inda ta shiga idanu su bita da kallo domin ta samu tabbacin cewa ta yi kyau ta kuma iya daukar hankali. Ko kun san cewa yawan shafe-shafe na bata kyaun fatar ‘ya mace? Domin yaye irin wadannan matsalolin shi yasa a yau na kawo muku yadda za a yi kyau ba tare da an yi kwalliya ba ko kuma an yi wani shafe-shafe ba.
· Hanya ta farko ita ce mace ta kasance mai yawan shan ruwa a koda yaushe. Koda kuwa sanyi ake yi. Domin yawan shan ruwa na wanke maikon da ke haifar da kurarrajen fuska.
· Mace ta kasance mai shafa mai a duk lokacin da ta yi wanka koda kadan ne. Ta shafa a fuska da wuya da hannu da kuma kafafunta domin wadannan wuraren ne suke fara nuna alamun tsufa a jikin mace.
· A kasance ana wanke fuska da sabulun wanke fuska a kullum safe da yamma. Yin hakan na wanke ragowar kwalliyar da aka yi.
· Kada a manta wanke gashin kai da man ‘shampoo’ kamar sau biyu a sati. Zama da gashi mai datti na sanya amosanin ka da yawan kaikayi a duk inda mace ta shiga da kuma wari.
· Kada a manta da amfani da man ‘sunscreen’ a kullum domin wannan man na dauke ne da sinadaren da ke kare kunan rana a fuska da kuma kare fuska daga kodewa ko kuma fesowar kuraje.
· A kasance ana shan ruwan dumi da lemon tsami a ciki kullum da safe kafin a ci komai. Yin hakan na karawa mace shekin fata da kuma sulbi.
· Yin wanka da sabulu yana fitar da daudar jiki wadanda suka makale kuma suna hana ramukan gumi fitowa. Yin wanka kullum ya zama wajibi a wajen mace.