Yadda za ki yi wanka don rage gajiya a damina

Yanzu da damina ta shigo, don haka ya kamata mu san irin ruwan da za mu yi wanka da shi. Sau da yawa za a ga wasu kuraje na feso wa mutum musamman a lokacin damina. Irin hakan na faruwa ne saboda wasu sukan yi wanka da ruwan sama. Ya kamata fatar mace ta kasance […]

Yadda za ki yi wanka don rage gajiya a damina
Yadda za ki yi wanka don rage gajiya a damina

Yanzu da damina ta shigo, don haka ya kamata mu san irin ruwan da za mu yi wanka da shi. Sau da yawa za a ga wasu kuraje na feso wa mutum musamman a lokacin damina. Irin hakan na faruwa ne saboda wasu sukan yi wanka da ruwan sama. Ya kamata fatar mace ta kasance mai laushi da kuma santsi.
A wannan makon mun  kawo miki wadansu sinadirai da za ki sa a cikin ruwan wankanki don rage gajiya da kuma samun fata mai laushi a lokacin damina.
Sinadirai:
·         Sabulu marar kamshi, ko sabulun jarirai (baby soap).
·         Man rosemary
·         Ruwa
·         Man rose water
·         Man glycerin.
 Za ku iya samun wadannan sinadarai a shagunan da sayar da mayukan kwalliya.
Amfanin sinadirain
·         Man rosemary na magance rikewar jijiyoyi kuma na kara karfin jiki.
·         Man glycerin na sanya fata ta yi santsi musamman ga mai gautsin fata.
·         Sabulu marar kamshi ko sabulun jarirai na cire dattin jiki.
·         Turaren banilla na sanya ruwan wanka ya yi kamshi.
Hadi
·         Ki dauki sabulu daya sai ki sanya shi cikin kwalba, sannan ki sanya man glycerin a cikin kwalbar. Ki girgiza kwalbar har sai sabulun ya narke, daga nan ki bar hadin na tsawon minti biyu zuwa uku.
·         Sai ki zuba ruwa a cikin hadin., daga nan ki diga man rosemary.
·        Bayan nan sai ki zuba turaren banilla  a cikin hadin don ki samu kamshi mai kayatarwa.
Bayan kin gama wanka, sai ki zuba ruwan dumi a jikinki domin wanke kumfar da ke jikin fatarki.