Yadda za ku duba sakamakon jarabawar NECO 2020 cikin sauki

Hukumar Shirya Jarabawa ta Najeriya (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala makarantar sakandare na 2020 a ranar Laraba 13 ga Janairu, 2021. NECO ta ce a sakamakon jarbaawar ta SSCE an samu karin kashi 2% na daliban da suka samu akalla ‘credit’ biyar, da suka hada da darussan Lissafi da Harshen Turnaci. Tashar Buhari: […]

Yadda za ku duba sakamakon jarabawar NECO 2020 cikin sauki

Hukumar Shirya Jarabawa ta Najeriya (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala makarantar sakandare na 2020 a ranar Laraba 13 ga Janairu, 2021.

NECO ta ce a sakamakon jarbaawar ta SSCE an samu karin kashi 2% na daliban da suka samu akalla ‘credit’ biyar, da suka hada da darussan Lissafi da Harshen Turnaci.

Ga matakan da za ku bi domin duba sakamakon jarabawarku cikin sauki:

  • Ziyarci shafin duba sakamakon jarbawar NECO, wato https://www.neco.gov.ng
  • Zabi shekarar da ka rubuta jarabawar. Misali, 2020.
  • Zabi irin jarabawar da ka rubuta. Misali, SSCE INTERNAL (JUN/JUL).
  • Sanya lambar sirrin da aka ba ka a wurin da bayar.
  • Cike lambar rajistarka ta jarabawar a wurin da ya dace.
  • Daga nan sai sai ka latsa maballin ‘check result’.
  • Bayan haka sakamakon jarabawarka zai bayyana.

Wadannan su ne matakan duba sakamakon jarabawar NECO a saukake.

Muna addu’ar Allah Ya sa a dace.