Yadda za ku ribaci ranaku 10 na farkon watan Zul-Hijjah
Kwanakin dai sune mafiya daraja a duk kwanakin shekarar Musulunci.
A yayin da muka shiga watan Zhul-Hijjah, malaman addinin Musulunci na ci gaba da kira ga Musulmai kan yadda za su ribaci falalar kwanakin 10 na farkon watan yadda ya kamata.
A cikin wannan hudubar ta Juma’a, Imam Murtada Gusau, Babban Limanin Masallacin na Nagazi-Uvete da masallacin marigayi Alhaji Abdurrahman Okene da suke Okene a Jihar Kogi, ya yi bayani a kan wasu daga cikin falalolin wadannan kwanakin guda 10.
- Mukabalar Kano: Za a gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu
- ’Yan bindiga sun sace sarki da iyalansa 12 a Kaduna
Ku biyo mu:
Bayan haka ya bayin Allah! Daga cikin muhimman lokutan yin ibada akwai ranaku 10 na farkon watan Zul-Hajji, ranakun da Allah Ya fifita a kan sauran ranaku na shekara. Ibn Abbas ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Babu wani aiki da ya fi alheri irin wanda aka yi a ranaku 10 na farkon Zul-Hajji.”
Sai wadansu sahabbai suka ce: “Ko da jihadi a tafarkin Allah?” Annabi (SAW) ya ce: “Ko da jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya tafi da kansa da dukiyarsa bai dawo da komai ba.”
(Buhari). Kwanaki goma manya ne kuma mafiya soyuwa a wurin Allah. Ibn Umar (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Babu wasu ranaku da suke da girma kuma suka fi soyuwa a wurin Allah fiye da ranaku goma na farko Zul- Hajji. Don haka, ku yawaita tahlili da takbiri da tahmidi a cikinsu” (Musnad Imam Ahmad).
Daga cikin darajojin ranaku 10 na Zul-Hajji akwai:
- Allah Ya yi rantsuwa da ranakun goma a cikin Alkur’ani inda Ya ce: “Ina rantsuwa da alfijiri. Da darare goma.” (Q:89:1-2). Magabata da suka haxa da Ibn bbas (RA) sun ce darare goma da aka ambata a cikin Alqur’ani su ne darare goma na farkon Zul-Hajji.
- Annabi (SAW) ya ce dararen goma su ne ranaku mafiya alheri na shekara kamar yadda muka ambata a baya.
- Su ne ranaku mafiya alheri na yawaita ambaton Allah, kamar yadda Hadisin da ya gabata ya nuna.
- Sun kunshi Ranar Arfa (9 ga Zul-Hajji) wadda a cikinta Allah Ya cika addini. Kuma yin azumi a cikin ranakun yana kankare kananan zunuban shekarar da ta gabata da wadda ake ciki, (manya suna buqatar tuba da mayar da hakki ga mai shi).
- Sun kunshi Ranar Hajji Mafi girma wato Ranar Layya, kuma wannan rana ita ce mafi girma a daukacin shekara.
Don haka, ku yawaita karatun Alkur’ani a cikinsu, ku yi sallolin nafila da Kiyamul Laili da sadaka da yada ilimi da tuba ga Allah.
Ku yawaita fadin Astagfirulla, ku yi azumi ku Kaurace wa haram da fadin haram da sauraren haram da sauransu. Haka kuma ku yi addu’o’i ga al’ummar Musulmin duniya.Ku yi gaggawar ribatar ranakun kafin lokaci ya kure muku.
Kazalika, ana so Musulmi ya yawaita sadaka da sada zumunci da azumtar wadannan kwanakin da yi wa kai hisabi tare da duk wani aiki da mutum ya san na alheri ne wanda zai kara kusantar da shi zuwa ga Allah.
Imam Murtada Gusau, Babban Limanin Masallacin Juma’a na Nagazi-Uvete da masallacin marigayi Alhaji Abdurrahman Okene da suke Okene a Jihar Kogi.