……Yadda za mu magance magudin zabe a 2015 -Dokta Ahmad

A lokacin Tafsirin da Dokkta Ahmad Gumu yake gabatarwa a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, ya yi bayanin matakin da suke son dauka domin kawo karshen magudin zabe a kasar nan, Aminiya ta tuntube shi domin jin karin bayani. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Ko za ka yi mana karin bayani a kan […]

……Yadda za mu magance magudin zabe a 2015 -Dokta Ahmad
……Yadda za mu magance magudin zabe a 2015 -Dokta Ahmad

A lokacin Tafsirin da Dokkta Ahmad Gumu yake gabatarwa a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, ya yi bayanin matakin da suke son dauka domin kawo karshen magudin zabe a kasar nan, Aminiya ta tuntube shi domin jin karin bayani. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ko za ka yi mana karin bayani a kan zancen tara kudi domin samar da ingantaccen zabe a kasar nan?
Gumi: Abin da na ce shi ne, idan ka duba matsalar da ke kasar nan ga ba daya matsala ce ta shugabanci. To , abin da shagabanni suke fuskanta shi ne mutane ba su amince da su ba, domin mutane na ganin ta hanyar magudi suka hau mulki, saboda haka babu wanda ke sauraransu. Ina ganin wannan shi ne abun, idan muka inganta hanyar zabe ya zama an yi zabe wanda ya ci zabe an ba shi, kuma mutane sun amince shi ya ci, wannan mutum idan ya ce ku tashi tsaye mutane za su tashi, idan kuma ya ce ku zauna za su zauna.
Duk rikice-rikicen nan da muke fama da su da muna da shugabannin da mutane suka yarda da su da duk ba su taso ba. Ashe tashe-tashen hankali da rashin da’a da komai, rashin shugabanni ne ke haifar da su. Saboda haka muka gane cewa zabe idan za a yi shi da gaskiya a bai wa wanda ya ci, da an samu zaman lafiya a kasar nan.
Mun ga a kasashen duniya inda ake zabe kamar Indiya, inda mutum miliyoyi suka yi zabe kuma da aka kayar da jam’iyya mai mulki masu mulki suka ce an kayar da mu, domin suna yin komai a bayyane. Mu a nan komai a boye ake yi, hatta yakin da ake yi da ta’addanci a boye ake yi, ba za ka taba ji an ce gashi an kama wani an nuna shi domin a gane daga wani kabila ko addini yake ba, komai a boye ake yi. Idan komai a boye ake yi, saboda haka akwai tuhuma, ba mu yarda da kowa ba. Wannan ya sa muke son yin amfani da wadansu abubuwa biyu, watau sauki da Allah Ya

Kawo domin fita daga wannan kangi. Ba wai wani dan takara za mu taimakawa ba, duk ‘yan takaran za mu taimaka wa.
Abin da za mu yi shi ne, za mu yi tsari yadda ake yinsa a duniya. Yanzu dai doka ne cewa duk inda aka yi zabe a wurin za a kidaya kuri’u a kafa a bango domin kowa ya gani, amma matsalar ita ce, idan aka kafa na garinku ko kauyanku ai ba ka san na kauyan da ke kusa da ku ba, shi ya sa za a iya magudi a kuma yi cuta. Amma yanzu Allah Ya yi na’urar  Intanet. Idan muna da tsari sai mu sanya wakili a kowace mazaba.  Shi wannan wakili ba na wata jam’iyya ba ne, wakili ne na masu kula da zabe. Ana kafa wannan sakamako a bango, wanda doka ne a kafa, kuma yana cikin doka cewa ya zama hakkin kowa ya gani, kuma dan sanda bai isa ya hanaka gani ko daukar hotonsa ba. Idan aka dauki hotonsa mun samu wadansu kwararrun mutane ‘yan Najeria ‘yan uwanmu a Amurka da suka bayyana mana cewa idan har za mu iya aika musu da hotunan wadannan zabubbuka shi ke nan sun gama mana aiki. Nan take za ku rika ganin na’urorin  sun canza hoton zuwa rubutu. Daga nan ne za mu gane dan takara kaza na jam’iyya kaza shi ya lashe zabe a mazaba kaza. Idan aka hada mazabun za a gane shi ya lashe a jaha kaza. Amma amfaninsa kuma ko da ba mu iya tara kudin da za mu iya daukar mazaba dubu dari da hamsin ba, zai zamanto mafi yawansu muna iya yi.
•    Ko ta haka zai iya hana yin magudi a zaben shugaban kasa, domin sharadin zaben shugaban kasa shi ne, sai ya lashe kashe biyu cikin uku a kasa. Wannan biyu cikin ukun nan idan ka tsare ta ka tabbata bai samu kashi biyu na kariya da ake magana ba, kun tsare al’umma. Kwanan nan aka yi zabe a Turkiya mun ga haka, domin shugaban kasar kamar kowa zama ya yi yana jiran sakamako, kuma duk duniya tare muka ga sakamakon da su.  Shi ne tsarin da muke so muma mu yi, domin gwamnati ko an ce ta yi za a ce sai an aika da kuduri majalisa da sauransu. Shi ne muka ce yanzu ku jama’a abin na hannunku. Ku kawo kudi a biya wadannan jami’ai, kuma kudin za a kashe su ne a wajen sayen intanet da  kamarori masu dauke da intanet da kuma  ga jami’an da za su mayar da wannan ilmi zuwa   internet . Wadannan jami’ai kuma a Amurka suke zaune, ‘yan Najeriya ne ‘yan uwanmu, a can za su bude dakin aiki, inda ba za a dauke hoto ba balle a yi magudi. Daga nan intanet idan ka bude za ka ga yadda ake zabe a unguwar Sarki da sauran wurare. Haka muka yi tsarin, amma abin na bukatar kudi masu yawa kuma. Kowa ya kawo nasa gudunmuwa na duk abin da zai iya.
Aminiya: Wannan tsarin za ku mayar da hankali ne a Arewa ne kawai ko har da sauran yankunan kasar nan?
Gumi: Kowa ne, har da ma wadanda ba musulmi ba idan suna son ‘yanta kansu suna iya bada taimako. Tsari ne na duk ‘yan Najeriya. Ba taimako ba ne ga wani dan takara daya ba, a’a ga ‘yan Najeriya ne duka. Domin duk lokacin da ‘yan Najeriya ke zaben mutanen da suke so za a samu kwanciyar hankali. Saboda shugaban da suka zaba idan ya ce  su bar abu dole su bari, amma idan wanda suke ganin ya murde zabe ne ya hau, ko ya yi musu magana zaginsa kawai za su yi.
Aminiya: Idan na fahimce ka, ke nan ba kudi za a bai wa wani dan takara ba, kayan aiki za a saya da kudin?
Gumi: Kayan aiki za a saya, mafi karanci kowace mazaba za a ajiye mutum biyu, ka ga ke nan muna bukatar mutum dubu dari uku. Mutanen nan kuma dole sai ka ba su kudin mota da abin da za su ci, sannan sai mun kashe kudi wajen sayen intanet da za a aika sakamakon zaben. Kudin ne muke bukata wajen jama’a domin su ‘yanta kansu da kansu. In dai talakan Najeriya yana son ‘yanta kansa yanzu Allah Ya kawo lokaci. Daga Naira dari,  idan har dukkanmu miliyoyin nan  za mu tara wadannan kudade  muna da abin da za mu ‘yanta kanmu, mene ne ‘yanta kanmu? wanda ya ci zabe a ba shi.
Aminiya:  Wa za a bai wa kudin ya ajiye?
Gumi: Yanzu haka a masallaci mun kafa kwamiti, su ma sauran mutane sai su kafa nasu kwamitin, idan kuma ‘yan kasuwa ne su ma sai su kafa kwamiti, idan tasha ce, ita ma sai su kafa kwamiti su nada wani amintacce a wajensu, su rubuta kudinsu duk su hada su kawo, sai su kai masallacin Sultan Bello.
Aminiya: ’Yan kwamitin sun fara aiki ke nan?
Gumi: Eh, sun fara aiki, a ranar farko sun tara Naira dubu ashirin da biyar, daga yanzu har zuwa zaben  2015 kungiyoyi da kowa da kowa su daure su tara kudinsu. ‘Yanta ku za a yi. Za mu iya cewa wadanda suka tara wannan kudi suka kuma bai wa amintaccensu za a bashi rasiti da ke nuna ya kawo wannan kudi, sannan kuma wannan kudi za mu rika buga shi domin kowa ya sani. Kuma kowa ya san cewa babu abin da ake yi a boye.
Dama abin da ya kashe mu a kasar nan shi ne yin abubuwa a cikin sirri, to yanzu muna son koya wa ‘yan siyasa cewa komai a bayyane ake yinsa. Abin da kawai muke so daya ne, wanda ya ci zabe kawai a ba shi, kada a yi magudi.
Aminiya: Kana ganin wannan tsari shi ne maslaha?
Gumi: Mun yi tunani babu wani tsari, domin idan ka ce za ka jira gwamnati ba za’a yi ba, idan kuma ka jira ‘yan siyasan su ma ba za su yi ba, abin da ya rage shi ne su talakawan su kawo kudi, ga shi Allah ya kawo sauki. Saukin cewa ana kafawa tun daga mazaba, sauki na biyu, ana iya dauka a saka a intanet duniya ta gani, ba a Najeriya kadai ba. Wannan saukin sai mun kashe kudinmu a kai domin duk ya wadatar da mu. Muna zaune a gidanmu za mu ga wanda ya ci zabe.