Yadda za mu tabbatar da canji –Ministoci
A ranar Laraba da ta gabata ce Shuagban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ministocin gwamnatinsa su 36, inda daga nan kowannensu ya nufi ma’aikatar da aka tura shi domin fara aiki. Bikin kaddamarwar, wanda ya gudana a dakin taro na gidan gwamnati a Abuja, ya zama taro na farko da shugaba Buhari ya yi […]

A ranar Laraba da ta gabata ce Shuagban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ministocin gwamnatinsa su 36, inda daga nan kowannensu ya nufi ma’aikatar da aka tura shi domin fara aiki.
Bikin kaddamarwar, wanda ya gudana a dakin taro na gidan gwamnati a Abuja, ya zama taro na farko da shugaba Buhari ya yi da ilahirin ministocin da za su jagoranci manyan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya.
Mafi yawa daga cikin ministocin dai sun nuna kakkarfar niyyar aiki tukuru domin ganin cewa an samu canjin da talakawa suke da tsimaye.
Rotimi Amaechi, tsohon Gwamnan Jihar Ribas, shi ne aka mika wa Ma’aikatar Sufuri a matsayin Minista. Ya bayyana cewa zai gudanar da aikinsa bisa jajircewa da kula, ta yadda ba zai daga wa barayi kafa ba. Ya ce duk wani jami’in gwamnati a ma’aikatarsa da ya zabi ya yi almundahana da dukiya, ba zai sha da dadi ba, muddin aka kama shi.
“Ni ba lalatacce ba ne, kamar yadda ’yan adawata suke yi mani ikirari. Nakan tafiyar da aikina ne bisa ka’ida da bin hanyar da ta dace. Ba na bayarwa kuma ba na amsar rashawa. Idan har kana son yin mu’amala da ni, to kada ka sake ka ba ni kudi. Ni ma kaina ba zan taba mika maka kudi da sunan hanci ba. Ni ina tsoron tafiya jarun, don haka ba na sata, kuma tabbas ba zan taba kyale barawo ba.” Abin da ya gaya wa ma’aikatan da ke ma’aikatarsa ke nan, a yayin da ya gana da su a karon farko.
A yayin da Babban Sakatare a ma’aikatar, Alhaji Sabi’u Zakari, ya mahabarci sabon minista Amaechi, Ministan ya yi wa daraktoci da sauran ma’aikata jawabi, inda ya bayyana masu irin yadda zai gudanar da aikinsa. Ya ce ba zai yi shiri da malalata ba, masu kyuyar zuwa aiki ko kuma wadanda ke zuwa a makare ba. Amma ya nemi ma’aikatan da su jajirce, su nuna kwazo, ta yadda za a yi aikin da zai bunkasa kasa.
Shi kuwa Ministan Al’amuran Noma da Bunkasa Karkara, Cif Audu Ogbeh, a yayin da yake kama aiki jiya a Abuja, ya ce zai maida hankali ne wajen bincike da bunkasa harkokin saye da sayar da amfanin gona. Ya ce ta haka ne za a rage matsalolin da ke fuskantar sashin noma na kasar nan.
Kamar yadda ya ce, a duk shekara Najeriya na asarar Naira biliyan 22 wajen shigo da kayan abinci daga kasashen waje, wanda idan aka bunkasa harkar noma a gida, za a toshe wannan gibi da ake wa tattalin arzikin kasa, kuma hakan zai samar da ayyukan yi ga ’yan kasa.
A nasa bangaren kuwa, sabon Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Folorunso, alkawari ya yi na kawo canje-canje masu amfani a harkar lafiya a kasar nan, musamman yadda za a samu biyan bukata ta wanna fuska a fadin Najeriya.
Ministan ya fadi haka ne a yayin da yake kama aiki a Larabar da ta gabata, jin kadan da rantsar da shi. “Akwai wasu sauye-sauye da dama da muke da bukatar kawowa. Za mu duba yadda za mu rika gudanar da ayyukanmu tare da manya da kananan sassan hukumomin lafiya, domin ganin mun kawo canjin da ake bukata na bunkasa harkokin lafiya. Don haka za mu yi aiki hannu-da-hannu tare da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi. Inji shi.
Kamar sauran takwarorinsa, shi ma Ministan Ma’aikatar Sadarwa, Barista Adebayo Shittu, a yayin da ya kama aiki, gargadi ya yi wa daukacin ma’aikatan da ke karkashinsa da cewa, dole ne kowa ya tashi tsaye, domin kuwa ba za a ci gaba da aiki yadda aka ga dama kamar yadda aka saba a baya ba.
“Ya zama dole mu amince da cewa, ba za a ci gaba kamar yadda ake yi a baya ba yadda aka ga dama. Za mu yi aiki ne kawai bisa tsarin da doka ta amince da shi. Za mu daraja ka’idar aiki bisa doka kuma za mu yi aiki bisa sadaukarwa ba tare da gajiyawa ba.
Labarin dai bai canja ba, a ta bakin Ministar Kula da Muhalli, Amina Mohammed da kuma karamin ministan ma’aikatar, Ibrahim Usman. A yayin da suke kama aiki, ministocin sun sha alwashin kawo canji, inda suka ce za su mayar da hankali kacokan wajen gyara da kyautata muhalli, tare da magance matsalolin da suka danganci gurbacewar muhalli a fadin kasar nan.
“kalubalen da ke gabanmu a kasar nan suna da yawa, don haka ya zama wajibi mu jajirce wajen tunkararsu da kawo magani. Domin kuwa ba za mu taba iya kawo canjin da ya kamata ba, idan muka ci gaba da gudanar da aiki ta tsohohuwar hanya,” inji Amina.
A nasa bangaren kuwa, sabon karamin Ministan albarkatun mai, Dokta Emmanuel Ibe Kachikwu, a yayin da yake kama aiki kuma a jawabinsa ga shugabannin sassan ma’aikatu na ma’aikatar tasa, ya ce: “Na tsara cewa nan da ’yan watanni, mun kammala zama tare da manajojin daraktocimu domin fahimtar da su tsarin da gwamnatin nan take so ta bi wajen kawo sauyi managarci a kasar nan. Za mu yi nazarinsu mu ga cewa ko za su iya aiwatar da abin da ake bukata. Ba kuma ina nufin za mu canza ko mu kori daraktocin ba ne, amma dai za mu bukace su da su yi aiki sosai, domin ganin cewa an samu bunkasar da ake so.” Ministan kuma ya ce lallai za su duba batun sassaucin farashin mai da kuma sabuwar dokar nan da ta danganci albarkatun man fetur (PIB) da ake ta kai-komo da batunta tun a gwamnatocin baya.
Ministan Ma’aikatar Watsa Labarai kuwa, Lai Muhammad, a yayin da ya kama aiki a Larabar da ta gabata, ya ce zai bi dukkan alkawuran da suka yi a yayin yakin neman zabe, domin ganin sun cika su. “Ina matukar farin ciki da aka zabe ni in yi hidima ga al’ummar kasar nan. Harkar watsa labarai na da matukar muhimmanci wajen tafiyar da harkokin gwamnati. Don haka za mu yi kokarin bin kadin dukkan alkawuran da muka yi a yayin yakin neman zabe, domin tabbatar da canjin da muka yi alkawarin kawowa na bunkasa kasa.”
Tuni dai daukacin ministocin suka kama aiki a ma’aikatunsu daban-daban. Ko za su iya cika alkawari na kawo canjin kamar yadda suka alkawurta? Lokaci ne kadai zai tabbatar da haka.